Kungiyar ASUU ta shiga dogon tattaunawa da Gwamnatin Buhari a Abuja

Kungiyar ASUU ta shiga dogon tattaunawa da Gwamnatin Buhari a Abuja

- Shugabannin ASUU sun shiga taro da na Gwamnatin Tarayya a Abuja

- An soma wannan taro ne tun karfe 5:00 na yammacin ranar Alhamis

- Gwamnati tana kokarin kawo karshen yajin-aikin da ake yi a Jami'o'i

A ranar Alhamis, 18 ga watan Disamba, 2020, mu ka ji cewa wakilan gwamnatin tarayya da shugabannin kungiyar ASUU sun shiga wata ganawa.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa an soma wannan doguwar tattaunawa ne tun karfe 5:13 na yamma.

Ministan kwadago da samar da aikin-yi na kasa, Chris Ngige, ya kira wannan zama bayan a baya an yi ta dakatar da wannan taron da aka shirya za ayi.

Kafin a zauna, Dr. Chris Ngige ya bayyana cewa gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta yi duk abin da za ta iya domin ganin an janye yajin-aiki.

KU KARANTA: Gwamnati ta fasa zama da ASUU

ASUU ta maidawa Ministan raddi bayan ya zargi malaman jami’an kasar da laifin gaza shawo karshen wannan yajin-aiki da aka shafe watanni tara ana yi.

Majiyar ba ta bayyana lokacin da aka kammala wannan taro ba, amma an dauki tsawon lokaci ana tattaunawa tsakanin bangaren ASUU da na gwamnati.

Ana sa ran cewa gwamnatin tarayya za ta shawo kan malaman jami’a su janye yajin-aikin da su ka tafi tun watan Maris, wanda hakan ya hana yara karatu.

Sau biyu ana shirya za ayi wannan zama amma aka rika dakatarwa, a karshe gwamnatin tarayya ta fito ta ce ta fasa zama da shugabannin malaman jami’ar.

KU KARANTA: Gwamnati ba ta cika alkawarinta ba - ASUU

Kungiyar ASUU ta shiga dogon tattaunawa da Gwamnatin Buhari a Abuja
Wakilan Gwamnati da Kungiyar ASUU Hoto: dailytrust.com
Source: Facebook

A zaman da aka yi ranar 27 ga watan Nuwamba, gwamnati ta yi alkawarin za ta biya malaman jami’a N70 a matsayin alawus da kudin gyaran jami’o’i.

Makonni uku kenan kungiyar ASUU ba ta ce komai ba bayan wannan tayi da aka yi mata. ASUU ta ce sai ta tuntubi ‘ya ‘yanta kafin ta iya janye yajin-aikin.

A baya kun ji yadda kungiyar malaman jami'a ta ASUU ta gindaya wa gwamnatin tarayya sabon sharadin komawa aiki bayan rufe makarantu tun Maris.

Shugaban ASUU ya ce ba za su janye yajin aiki ba sai gwamnati ta biya su duk albashin da ta rike.

An rahoto Farfesa Biodun Ogunyemi ya na cewa babu yadda za a yi malamai su koma makarantu a cigaba da daukar darasi yayin suna cikin yunwa da fatara.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Online view pixel