2023: Lokacin Ibo ya yi inji Anyim, Nwodo, Onu da Ukiwe a babban taron Inyamurai

2023: Lokacin Ibo ya yi inji Anyim, Nwodo, Onu da Ukiwe a babban taron Inyamurai

-Wasu manyan kasar Ibo sun yi taron Duniya a cikin karshen makon nan

-Ibo sun cin ma matsaya cewa lokaci ya yi da zasu dare kan ragamar mulki

-Kungiyar tana so a gyara doka yadda Inyamuri zai karbi Najeriya a 2023

Fitattun kabilar Ibo sun fara fafatuka na ganin yankinsu ya samu mulkin Najeriya a 2023, Vanguard ta fitar da wannan rahoto a farkon makon nan.

Wadannan manyan kabilar Ibo suna neman ‘yan Najeriya su mara masu baya, domin a cewarsu lokaci ya yi da shugaban kasa zai fito daga cikinsu.

‘Ya ‘yan kabilar sun bayyana wannan ne a babban taron Duniya da su ka yi a Abia. Wannan shi ne karo na shida da aka gudanar da irin wannan taro.

Tsohon mataimakin shugaban kasa na soja a lokacin Janar Ibrahim Babangida, Ebitu Ukiwe (mai ritaya), ya jagoranci wannan zama da aka yi a jiya.

KU KARANTA: Okorocha ya na harin kujerar Shugaban kasa

Sauran wadanda suka halarci taron sun hada da Nnia Nwodo, Dr. Ogbonnaya Onuh, Anyim Pius Anyim, Iyom Josephine Anenih, da Dr. Ifedi Okwenna.

Jaridar Vanguard ta ce Farfesoshin da su ka halarci zaman sun hada da Ike Nwachukwu, Joe Irukwu, George Obiozor, Ihechukwu Madubuike, da Greg Ibe.

A karshen taron, an tsaida masa cewa jam’iyyiun siyasa su kai takara zuwa yankin Kudu maso gabashin Najeriya a zaben 2023, domin Ibo ya yi mulki.

Sannan kungiyar ta bukaci ayi wa tsarin gudanar da Najeriya garambawul domin a samu cigaba.

KU KARANTA: Sanata Abaribe ya ce Ibo sai ya yi mulki

2023: Lokacin Ibo ya yi inji Anyim, Nwodo, Onu da Ukiwe a babban taron Inyamurai
Manyan Ibo a fadar Shugaban kasa Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

A wannan taro na kwana biyu, manyan Ibon sun amince da cewa ‘yan majalisar yankinsu, su bijiro da maganar tsarin kama-kama wajen shugabancin Najeriya.

Tun a watannin baya kuka ji cewa wasu kungiyoyin Ibo sun fara buga tamburan yakin neman zaben 2023, suna sa ran cewa a zaben 2023, su karbi mlkin kasar nan.

Wasu manyan yankin su na da ra'ayin cewa ya kamata Ibo ya yi mulki don Najeriya ta dinke.

Rabon mutumin Ibo da rike Najeriya tun Janar Aguiyi-Ironsi a shekarar 1966. Kabilar mai mutane fiye da miliyan 25 ta shafe shekaru kusan 60 ba ta ji kanshin mulki ba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel