Edo: Yadda muka tallafi Oshiomhole da dukiyarmu - Obaseki

Edo: Yadda muka tallafi Oshiomhole da dukiyarmu - Obaseki

Gwamna Godwin Obaseki na jihar Edo ya ce a lokacin da wanda ya gada, Adams Oshiomhole ya yi takarar gwamnan jihar a 2017, bashi da kudi.

Oshiomhole, tsohon shugaban kungiyar kwadago ta kasa wanda ya nemi kujerar gwamnan jihar Edo karkashin jam'iyyar AC ya sha mugun kaye a hannun Oserheimen Osunbor na jam'iyyar PDP.

Amma bayan kalubalantar nasarar Osunbor, kotu ta kwace karagar mulkin jihar tare da mika ta hannun Oshiomhole bayan shekara daya.

Edo: Yadda muka tallafi Oshiomhole da dukiyarmu - Obaseki
Edo: Yadda muka tallafi Oshiomhole da dukiyarmu - Obaseki Hoto: Vanguard
Asali: UGC

A yayin zantawa da manema labarai bayan mika fom din nuna ra'ayin takarar gwamnan jihar Edo a karkashin APC, Obaseki ya ce babban kuskure ne idan aka ce ya ci amanar Oshiomhole.

Gwamnan ya ce ba wai taimakon Oshiomhole ya yi kadai wurin zama gwamna ba, ya sadaukar da abubuwa masu tarin yawa don tabbatar da cewa ya zama shugaban jam'iyyar APC mai mulki.

"A rayuwa, kowa na samun taimako kuma kowa ana iya taimakonsa. Wanda kuke magana, ba shi da kudi a lokacin da ya bar kungiyar kwadago don neman kujerar gwamna. Mun san yadda muka yi ya zama gwamna," yace.

"Na sadaukar da shekaru takwas na rayuwata ina bauta masa a jihar Edo. A yanzu mun san abinda muka gina saboda mun fara gini mai kwari.

"Idan kuka yi maganar cin amana, mu gane. Ina so in tabbatar muku da cewa ina godiya garesa saboda ya taimaka min. Na san sadaukar wa da muka yi har ya zama shugaban jam'iyyar APC na kasa."

Obaseki, wanda yake yaki da Oshiomhole ya ja kunnen shugaban APC din na kasa a kan ya zuba ido ya ga yadda za ta kaya a zaben fidda gwani.

"Ina amfani da wannan damar wajen kira ga Kwamared Oshiomhole da ya tsame kanshi daga zabar wa Edo shugaba.

"Hakan ba adalci bane. Don haka ina shawartar shi da ya tsame kanshi ya kuma bar mu mu sasanta tare da gina jam'iyyar mu."

KU KARANTA KUMA: COVID-19 ta kashe hadimi a fadar gwamnan Gombe, an rufeta ana shirin feshi

Ya kara da cewa shekaru hudu basu ishe shi ba don haka ne yake bukatar wasu shekaru hudu don tabbatar da ayyukan ci gaban da yayi niyya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng