Farin jinin PDP, rikicin APC, gajiya da Oshiomhole, da yadda Obaseki ya zarce a kan kujerar Gwamna

Farin jinin PDP, rikicin APC, gajiya da Oshiomhole, da yadda Obaseki ya zarce a kan kujerar Gwamna

- Ba sabon labari ba ne cewa PDP ce ta yi nasara a zaben Gwamnan Jihar Edo

- Godwin Obaseki ya samu kuri’a 307,955, Osagie Ize-Iyamu ya na da 223,619

- Mun kawo wasu daga cikin abin da ya sa ake ganin APC ta gaza yin nasara

A zaben jihar Edo, ‘dan takarar PDP, Godwin Obaseki ya doke Osagie Ize-Iyamu na jam’iyyar APC mai hamayya a kananan hukumomi 13 a cikin 18 da ke jihar.

APC ta yi nasara ne kurum a yankin Owan da Etsako. Ita kuwa PDP ta yi galaba a Igueben, Ikpoba-Okha, Uhunmwonde, Yankunan Esan, Egor, Owan, Ovia, Oredo.

Godwin Obaseki ya doke APC a karamar hukumar ‘dan takararta Ize Iyamu watau Orhionmwon.

Me ya jawo APC ta sha kashi haka a wannan zabe bayan da ta na rike da mulkin jihar Edo?

Mun tsakuro maku wasu daga cikin wadannan dalilai daga jaridar The Cable:

KU KARANTA: Wanene Godwin Obaseki?

1. Karya Adams Oshiomhole

Godwin Obaseki da abokan aikinsa sun fito da nufin su yi raga-raga da tsohon gwamna Adams Oshiomhole wanda alakarsu ta cabe bayan 2016. Wannan sabani ya yi sanadiyyar rusa majalisar NWC ta APC da kuma hana Gwmnan mai-ci tikitin jam'iyya.

2. Sabuwar soyayyar Obaseki da Ize Iyamu

Mutanen jihar Edo sun marawa Obaseki baya ne a dalilin irin abubuwan da aka san Oshiomhole ya taba fada a baya game da Osagie Ize-Iyamu lokacin ya na PDP. Kwatsam kuma sai aka ji APC ta yi amai ta kashe, ta na tallatawa mutumin da ta soke shi a baya.

3. Bidiyon Bola Tinubu da Abdullahi Ganduje

Wani gajeren bidiyo da jagoran jam’iyyar APC, Bola Tinubu ya fito ya yi, ya na kira ga al’ummar Edo su bijirewa PDP a zaben bai taimaka ba, asali ma ana ganin wannan bidiyo sai dai ya fusata jama’a ta yadda su ka fita da fushin tika jam’iyyar APC da kasa.

Tun da APC ta nada Abdullahi Ganduje shugaban yakin neman zabe, wasu su ke zargin akwai yunkurin a hana zaben gaskiya, wannan ya sa mutane su ka farga.

Farin jini PDP, rikicin APC, da yadda Obaseki ya zarce a kujerar Gwamna
Obaseki ya sake doke Ize-Iyamu a 2020
Asali: UGC

KU KARANTA: PDP ta kawo Edo - INEC

4. Rikicin gidan APC

Ana zargin Oshiomhole da rike wuka da naman APC a jihar Edo, ta yadda tsohon gwamnan ya hana kowa ta-cewa don haka ya yi ruwa da tsaki wajen kakaba Ize-Iyamu.

Wannan abin da ya jawo irinsu Osarodion Ogie, Anslem Ojezua, Frank Okiye, da Matthew Iduoriyekemwen su ka yi wa APC zagon-kasa a wannan zabe da aka gudanar.

5. Karfi da karbar PDP

Jam’iyyar PDP ta taimakawa Godwin Obaseki wajen komawa kan kujerarsa duk da cewa ya sauya sheka ne ana daf da zaben fitar da gwani. ‘Ya ‘yan PDP sun hada kai a Edo, sannan manyan jam’iyyar hamayyar na kasa sun taya Obaseki yaki domin cin zaben.

A jiya kun ji cewa yayin da APC ta ke nuna ba ta yarda da wannan sakamako ba, shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya taya dan jam'iyyar PDP murnar lashe zaben.

INEC ta sanar da cewa gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki ne ya yi nasara da kuri'u mafi rinjaye.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel