Kaduna ta ce ta na tattaunawa da Pfizer da AstraZeneca kan kwayoyin COVID-19
- Gwamnatin Kaduna ta na kokarin ganin yadda za ta sayo magungunan Coronavirus
- An samu wasu kamfanoni a kasashen ketare da suka gano maganin cutar mashakon
- Nasir EL-Rufai yace jami’an gwamnatinsa sun ajiye magana da Pfizer da AstraZenca
Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya ce gwamnatinsa ta na magana da Pfizer da AstraZenca domin samun sayen magungunan COVID-19.
Mai girma Malam Nasir El-Rufai ya bayyana cewa ya na kokarin ganin yadda zai saye kwayoyin cutar COVID-19 miliyan daya daga wadannan kamfanonin.
Jaridar Daily Trust ta ce gwamnan ya bayyana wannan ne a lokacin da ya yi hira da gidajen rediyon jihar Kaduna a ranar Laraba, 16 ga watan Disamba, 2020.
Nasir El-Rufai ya ce tun watanni uku da su ka wuce su ka zauna da ma’aikatan kamfanin Pfizer domin ganin yadda za su mallaki magungunan wannan cuta.
KU KARANTA: COVID-19: Gwamna El-Rufai ya sake rufe gidajen rawa
Gwamnan yace Kaduna ta na cikin jihohi hudu ko biyar a Najeriya da suka nuna sha’awar sayen kwayoyin maganin da kamfanin Pfizer suka kirkiro kwana nan.
A cewar gwamnan, bai san adadin da za su bukata ba, “Sun fada mana cewa su na karbar oda ne daga Ingila da kasar Amurka, amma sun san da zamanmu”
Bayan haka, Malam El-Rufai yace sunyi magana da kamfanin kasar Birtaniya da Siwidin, AstraZenca, wanda su ma su ke aikin gano maganin COVID-19.
Gwamna El-Rufai yace maganin AstraZenca ya fi araha saboda za a iya adana shi cikin daki, ba kamar na kamfanin Pfizer wanda ke bukatar yanayi mai sanyi ba.
KU KARANTA: Najeriya ta fito da tsari na musamman domin maganin yunwa
AstraZeneca ba ta fara raba magungunanta ba, amma jihar ta na sa ran samun kwayoyi miliyan daya daga Afrika ta Kudu ko Kenya da zarar sun shiga kasuwa.
A ranar Alhamis ne ku ka ji Shugaban kasar Faransa, Emmanuel Macron ya kamu da Coronavirus, har ya shiga daki ya killace kansa na tsawon mako.
Bayan fama da kalubale wajen shugabannin kasashen Musulmai, Macron ya kwanta rashin lafiya, ya shiga cikin jerin shugabannin kasashen da cutar ta harba.
Kawo yanzu sama da mutane 59,300 su ka mutu sanadiyar cutar Coronavirus a kasar Faransa.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng