Buhari: Sojoji da Gwamna sun yi matukar kokari a kubuto da Daliban GSSS Kankara
- A ranar Alhamis aka ceto duka ‘Yan makarantar da aka sace a Jihar Katsina
- Shugaba Muhammadu Buhari ya yi jawabi jiya bayan an kubutar da Daliban
- Shugaban kasar yayi murna, ya godewa kokarin Masari da duk Jami’an tsaro
Shugaba Muhammadu Buhari ya tofa albarkacin bakinsa game da nasarar da aka samu wajen ceto ‘yan makarantar da aka sace a Kankara, jihar Katsina.
Mai girma shugaban kasar bayyana cewa gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari da Dakarun tsaron Najeriya sun yi kokari sosai wajen ceto ‘daliban.
A wani jawabi da ya fitar ta bakin Garba Shehu, a ranar Alhamis, 17 ga watan Disamba, 2020, ya ce dawowan yaran babbar sa’ida ce ga iyayensu da fadin kasar.
Muhammadu Buhari ya yi godiya da yadda mutanen Najeriya su kayi kokari wajen ganin an dawo da wadannan yaran makarantar sakandare zuwa gidajensu.
KU KARANTA: An ceto 'Yan makaranta 340 da aka sace a Katsina
Shugaban kasar ya roki jama’a su rika yi wa gwamnatinsa adalci yayin da ta ke yaki da fitinar rashin tsaro, rashin gaskiya da kuma matsalar tattalin arziki.
Buhari ya ce:
“Ina murnar fito da yaran da aka yi garkuwa da su a makarantar sakandaren kimiyya ta Kankara, wannan sa’ida ce ga daukacin Najeriya da kasashen Duniya.”
"Daukacin kasar nan ta na godiya ga gwamna Masari, jami’an leken asiri, sojoji da ‘yan sanda."
“Gwamnatinmu ta na sane da nauyin da ke kanta na tsare rai da dukiyoyin duka mutanen Najeriya.” Shugaban ya yi alkawarin ba zai yi kasa a gwiwa ba.
KU KARANTA: Satar Dalibai: Gwamnan Katsina ya yi karin bayani
A cewar Buhari, gwamnatinsa ta taka rawar gani wajen ceto wasu daga cikin ‘yan makarantar Chibok, da 'yan makarantar Dapchi sai kuma wannan karo.
Dazu kun ji cewa gwamnatin Katsina tayi karin haske a kan yaran makaranta da aka ceto, inda ta ce ba a biya ko ficika daga baitul-maki kafin a fito da yaran ba.
Masari ya bayyana cewa jam'an tsaro, kungiyar Miyetti Allah da hadiminsa ne su ka dage wajen ceto Yaran makarantar na GSSS Kankara da aka sace kwanaki.
Sannan, Rt. Hon. Aminu Masari ya karyata cewa yaran su na hannun 'yan ta'addan Boko Haram.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng