John Oyegun zai sulhunta rikicin Jam’iyyar APC a Kudu maso Kudancin Najeriya

John Oyegun zai sulhunta rikicin Jam’iyyar APC a Kudu maso Kudancin Najeriya

- Jam’iyyar APC ta na kokarin dinke barakar da ke cikin gidanta a Kudancin Najeriya

- An zabi John Odigie-Oyegun ya sasanta rigimar da ake yi a shiyyar Kudu maso Kudu

- APC ta fara shiryawa yadda za a karbe mulki daga hannun PDP a yankin a zaben 2023

Shugabannin rikon kwarya na jam’iyyar APC sun zabi John Odigie-Oyegun a matsayin wanda zai jagoranci kwamitin sulhun yankin Kudu maso kudu.

The Nation ta ce tsohon shugaban jam’iyyar mai mulki aka ba alhakin sasanta rigimar da ake yi a yankin.

APC ta sanar da wannan mataki da ta dauka ne ta bakin Lucky Imasuen, bayan wani taro da manyan jam’iyyar su ka yi a ranar 16 ga watan Disamba.

Lucky Imasuen zai zama sakataren wannan kwamiti na sulhu mai dauke da Sunny Jackson, Dr. Maryam Ali, Dr Sam Jaja, Clever Ikisikpo da Emmanuel Nsan.

KU KARANTA: Buhari ya na da niyyar alheri - Tinubu

Jagororin jam’iyyar ta APC sun amince za su hada-kai domin fita kunya a zabe mai zuwa na 2023.

Sanata John Akpanudoedehe ya jagoranci wannan zama da ya samu halartar John Odigie-Oyegun, da Ministoci; Rotimi Amaechi, Godswill Akpabio, Festus Keyamo.

Sauran wadanda su ka halarci wannan taron na APC su ne: Dr. Osagie Ehanire, Sanata Francis Alimikhena, Pastor Osagie Ize-Iyamu da kuma Great Ogboru.

A karshe, an cin ma matsaya cewa Akpabio, Amaechi, Sylva, Otega, Omo-Agege da sauransu, za su ajiye bambancinsu domin yankinsu ya samu mulki a 2023.

KU KARANTA: Siyasar Kano: APC za ta rasa ‘Yan Majalisa zuwa PDP bayan tsige Kakaki

John Oyegun zai sulhunta rikicin Jam’iyyar APC a Kudu maso Kudancin Najeriya
John Oyegun, Tinubu da Buni Hoto:punchng.com/tinubu-begins-apc-reconciliation-process-visits-oyegun
Source: UGC

Jiga-jigan jam’iyyar su ka tsaida magana cewa lallai bai kamata a rika samun rigingimun cikin gida a lokacin da wasu su ke kara shigowa cikin tafiyar APC a yankin.

A makon nan ne wani jigon APC a Arewa, tsohon gwamnan jihar Zamfara, Ahmad Sani Yarima, ya bayyana kudirinsa na tsayawa takarar shugaban kasa a 2023.

Sanata Yarima ya bayyana wannan kudirin nasa ne a ranar Laraba a Abuja, yace zai tsaya ne a karkashin jam'iyyar APC bayan wa'adin Muhammadu Buhari.

A cewar 'dan siyasar, babu wata yarjejeniyar da APC tayi na cewa 'yan kudu za su karbi mulki a 2023.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Online view pixel