Kashim Shettima: ‘Yan ta’addan Boko Haram sun kai wa Borno hari 2801 a bana

Kashim Shettima: ‘Yan ta’addan Boko Haram sun kai wa Borno hari 2801 a bana

- Tsohon gwamnan jihar Borno ya yi magana bayan an kai hari a Zabarmari

- Sanata Kashim Shettima ya ce sau 2800 ana kai wa jihar Borno hari a bana

- Shettima yana ganin Hafsun sojin kasa sun gaza, Buhari ya maye gurabensu

Kashim Shettima, tsohon gwamnan jihar Borno, ya na cikin wadanda suka mike a majalisar dattawa, suka koka game da sha’anin tsaro a makon nan.

Sanata Kashim Shettima ya yi Allah-wadai da kisan manoma 67 da ake zargin an yi a garin Zabarmari. Shettima ya ce garin bai da nisa da Maiduguri.

A cewar Kashim Shettima, abin da ya faru a kauyen Zabarmari, yana cikin mafi munin hari da ‘yan ta’addan Boko Haram suka yi tun da suka fara ta’adi.

Yayin da ya mike ya na jawabi kamar yadda wani bidiyo da ya shigo hannunmu ya nuna, Sanatan na Borno ya jero irin ta’adin da Boko Haram suka yi masu.

KU KARANTA: Sultan ya fito ya na Wayyo-Allah da halin rashin tsaro a mulkin Buhari

Shettima ya tuna wa majalisar dattawa cewa an kai wa matafiya hari a farkon shekarar nan a garin Auno, wanda hakan yayi sanadiyyar mutuwar rayuka 40.

Bayan haka, ‘yan ta’addan na Boko Haram sun hallaka wasu mutane 10 a garin Gubio a watan Yuni. Duk wadanda aka rasa a harin, masu fararen kaya ne.

Sanata Shettima ya kuma tado harin da aka kai a Lawanti, wanda ya kashe mutane 40. Har ila yau, kwanaki an je an kashe wasu manoman rani 20 a Maiduguri.

“Daga ranar 1 ga watan Junairu zuwa 19 ga watan Nuwamba, 2020, ‘Yan Boko Haram sun kai hari sau 2801 a jihar Borno” inji Sanata mai wakiltar tsakiyar jihar.

KU KARANTA: Fafaroma ya yi wa Boko Haram da su ka kai hari a Zabarmari addu’a

Kashim Shettima: ‘Yan ta’addan Boko Haram sun kai wa Borno hari 2801 a bana
Kashim Shettim da Buhari Hoto: pulse.ng
Source: UGC

Ya ke cewa: “Hafsun sojoji ba su yin abin da ya dace, idan har kuwa shugaban kasar ba ya tunanin haka, to ya gaza. Ba na addu’ar haka ne, ina fata ba haka bane.”

A makon nan kun ji cewa Gwamnonin Jihohi 36 za su yi wani zama a dalilin matsalar rashin tsaro, kamar yadda aka tsara, an yi wannan zama a ranar Talata.

Kungiyar NGF ta zauna a ranar Laraba bayan harin Zabarmari, ta ce matsalar rashin tsaro da ake fama da shi ya fi karfin jami'an tsaro, don haka sai an tashi-tsaye.

Wannan hare-hare zasu jawo karanci da tsadar abinci, wanda hakan zai kai ga taba tattalin kasa.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit Newspaper

Online view pixel