Satan yara: Gwamnati ta karyata batun biyan kudin fansa, da hannun Boko Haram

Satan yara: Gwamnati ta karyata batun biyan kudin fansa, da hannun Boko Haram

- Gwamnatin Katsina tayi karin haske a kan yaran makaranta da aka ceto

- Gwamna Aminu Bello Masari ya ce ba a biya kudi kafin a fito da yaran ba

- Rt. Hon. Aminu Masari ya karyata hannun Boko Haram a wannan ta’adi

A ranar Alhamis, 17 ga watan Disamba, 2020, gwamna Aminu Bello Masari ya tabbatar da cewa an saki daliban GSSS Kankara da aka sace.

A cewar gwamnan, shugabannin kungiyar makiyaya na MACABAN/Miyetti Allah su ka shiga, su ka fita wajen ganin wadannan yara sun kubuta.

Jaridar Punch ta ce Mai taimakawa Mai girma gwamnan a kan sha’aninn tsaro, Mallam Ibrahim Katsina, ya tabbatar da wannan lamari a jiya.

Ibrahim Katsina ya ce: "Alhamdulillahi, an ceto yaran, su na Tsafe, jihar Zamfara. Amma gobe (ranar Juma’a) da safe mu karasa da su Kankara.”

KU KARANTA: An ceto Yaranmu da aka sace - Masari (Bidiyo)

Da ya ke magana da gidan rediyon DWTV Hausa a shirinsu na dare, Aminu Bello Masari yace ba a biya sisin kobo wajen ceto ‘yan makarantar ba.

Da aka tambayi gwamnan abin da suka bada, sai ya ce: “Ba mu biya wadanda su kayi garkuwa da su kudin fansar komai ba, tsurar sasantawa ce.”

“Sa’a daya da ya wuce, sojojin Najeriya da jami’an gwamnati da su ke tattaunawa domin ganin an kubutar da yaran da aka sace suka fada mana an fito da duka yaran makarantar.”

“Wadanda suka shiga tattaunawar sun hada da Hadimina, manyan sojoji, dakarun ‘yan sanda, da kungiyoyin Miyetti Allah, duk suna ciki.” Inji Masari.

Satan yara: Gwamnati ta karyata batun biyan kudin fansa, da hannun Boko Haram
GSSS Kankara, Katsina Hoto: guardian.ng
Source: UGC

KU KARANTA: Ba ni na ce ‘Yan makarantar da aka sace sun dawo ba - Tsohuwar Hadimar Buhari

Ya jaddada cewa: “Wadanda su ka sace yaran ba ‘yan ta’addan Boko Haram ba ne, ‘yan bindiga ne.”

Idan za ku tuna, gwamnan Zamfara, Bello Matawalle ya bayyana cewa yana cikin wadanda su ka yi ruwa-da-tsaki, kuma ba a biya kudi wajen dawo da su ba.

Da ya ke magana, mai girma gwamnan ya bayyana wa manema labarai cewa an fito da yaran ne daga garin Tsafe, jihar Zamfara da ke makwabtaka da Katsina.

Gwamnan jihar Katsina, Masari ya bada adadin daliban da aka yi garkuwa da su da 344.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Online view pixel