KARIN BAYANI: An sako daliban makarantar Kankara 344, gwamnan Katsina (Bidiyo)
Labarin dake shigo mana da duminsa yanzu na nuna cewa an sako daliban makarantar sakandaren kimiya dake Kankara akalla 340 yanzu.
Gwamnatin jihar Katsina ta sanar da haka.
Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya sanar da hakan a hirarsa da wani dan jaridan Aljazeera, Ahmed Idris.
"Kawo yanzu, an bamu dalibai 340, daga baya an kara da 4, yanzu akwai dalibai 344 dake hanyarsu ta zuwa Katsina yanzu," Masari ya bayyana.
Yayinda dan jaridan ya tambayesa shin su kenan ko akwai saura, Masari ya ce gaskiya sai sun dawo, amma yan bindigan sun ce sun saki dukkan yaran dake hannunsu.
"Sai sun dawo, sun ce mana sun saki dukkan yaran da ke hannunsu. Sai mun ji daga wajen iyaye ko akwai wanda bai ga dansa ba."
"Gobe zamu sani ko akwai saura," ya kara.
Kalli bidiyon:
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng