Gwamnati ta karyata rade-radin ceto Yaran Makarantar da aka sace a Katsina
- A yau ne aka rika yada jita-jitar ceto Daliban makarantar GSSS Kankara
- Gwamnati ta karyata wannan rade-radi, ta ce ba ta ceto yaran ba tukuna
- Tsohuwar Hadimar Shugaban kasa ta musanya cewa an kubuto da yaran
Wasu rahotannin da ba su tabbata ba, sun rika yawo a ranar Alhamis cewa an ceto duka ‘daliban makarantar GSSS Kankara da aka sace kwanan nan.
Majiya daga wani gidan talabijin Najeriya ya tabbatar da cewa wani babban jami’in gwamnatin Katsina ya ce an ceto wadannan dalibai fiye da 300.
Legit.ng Hausa ta yi bincike game da labarin, inda ta gano cewa babu gaskiya a wannan rahoto.
Haka zalika jami’an tsaron da ake rade-radin sun kubuto da wadannan yara, ba su tabbatar da lamarin ba, hakan ya nuna babu gaskiya a jita-jitar.
KU KARANTA: Boko Haram ta sace 'Daliban GSSS Kankara
Majiyar mu wanda wani babban jami’in gwamnati ne a Katsina, ya shaidawa ‘yan jarida cewa kawo yanzu ba a iya nasarar kubuto da wadannan yara ba.
Abike Dabiri Erewa ta na cikin wadanda suka fara yada wannan jita-jita a shafinta na Twitter, daga baya ta fito ta ce wasu ne su kayi wa shafinta kutse.
Ta rubuta: “Yaaaay. An ceto yaran nan 333 da aka sace a Katsina. Allhamdulilah! Gwamnatin Shugaba Buhari ta dawo da yaranmu. An dawo da yaran!”
Bayan ‘yan mintuna, shugabar hukumar ta NIDCOM ta ce sam ba ita ta yi wannan magana ba.
KU KARANTA: Ba Boko Haram su ka sace 'Yan makaranta ba - Masari
Wadannan yara da aka dauke a makarantar kimiyyar kwana ta gwamnati sun shafe kwanaki shida a hannun wadanda ake zargi ‘yan Boko Haram ne.
Dazu kun ji cewa 'Yan ta'addan kungiyar Boko Haram sun fito da wani bidiyo inda aka ga wasu daga cikin daliban makarantar GSSS Kankara da ka sace.
Shugaban kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau, ya maidawa gwamnati martani ne, ya tabbatarwa Duniya su ne su kayi gaba da 'yan makarantar.
Gwamnati da hukumomin tsaro sun ce yaran da aka sace su na raye cikin koshin lafiya, kuma za ayi duk abin da za a iya wajen maida su gaban iyayensu.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng