Kankara: Masari ya caccaki Shekau, ya ce 'yan makaranta na hannun 'yan bindiga

Kankara: Masari ya caccaki Shekau, ya ce 'yan makaranta na hannun 'yan bindiga

- Gwamnan jihar Katsina, Bello Masari, ya musanta maganar Shekau ta alhakin satar daliban GSSS Kankara

- Gwamnan ya ce ba za su amince da maganar wani dan ta'adda ba, don kowa ya san 'yan bindigan gargajiya ne suka sace yaran

- Ya fadi hakan ne a wata tattaunawa da gidan talabijin din Channels suka yi da shi, inda yace yana da ja a kan maganar Shekau

Gwamna Bello Masari na jihar Katsina ya ce wadanda suka sace daliban GSSS Kankara, masu garkuwa da mutane ne ba 'yan Boko Haram ba, Channels Tv ta wallafa.

Ya musanta maganar Shekau ne a ranar Laraba, inda yace kowa yasan cewa 'yan bindigan gargajiya ne suka sace dalibannan.

Bayan kwanaki kadan da wasu 'yan ta'adda suka sace daliban GSSS Kankara, sai ga wata murya ta fara yawo a kafafen sada zumuntar zamani, wacce take cewa, "Ni ne Abubakar Shekau kuma 'yan uwana ne suke da alhakin sace yaran Katsina."

Kankara: Masari ya caccaki Shekau, ya ce 'yan makaranta na hannun 'yan bindiga
Kankara: Masari ya caccaki Shekau, ya ce 'yan makaranta na hannun 'yan bindiga. Hoto daga @ChannelsTv
Asali: Twitter

KU KARANTA: Kankara: Ku dawo mana da yaranmu maza, Okonjo Iweala ga FG

Satar daliban da har yanzu ba a ga fiye da mutane 333 ba. Sai dai, Masari ya ki amincewa da maganar Shekau.

Kamar yadda Masari yace, "Daga yadda labarai suka zo mana, masu garkuwa da mutanen gargajiya ne suka sace daliban."

A tattaunawar da Channels tayi da shi, ya ce "Wadannan 'yan bindigan sune masu yawo a cikin dajin Zamfara da na jihar Kaduna. Ba za mu yarda da maganar wani dan ta'adda ba, har sai mun tabbatar."

KU KARANTA: Tsoron juyin mulki yasa Buhari ya kasa sallamar shugabannin tsaro, Sanata Hanga

A wani labari na daban, satar daruruwan daliban Kankara na jihar Katsina ya janyo alamomin tambaya a kan matsalar tsaro, wanda hakan ya rikita tunanin iyaye da dama, Daily Trust ta ce.

Daya daga cikin iyayen, Hajiya Marwa Hamza, wacce aka sace dan ta da jikanta a daren Juma'a, cikin GSSS Kankara, ta bayyana irin tashin hankalin da ta shiga.

A cewarta, "Ban taba shiga damuwa ba a rayuwata irin wannan. Na san yadda ake ji idan dan uwan mutum ya rasu, saboda na rasa mahaifina, kuma na san mutuwa dole ce, dole mutum yayi hakuri. Amma wannan ba kamar mutuwa bane, ba mu san halin da yaranmu suke ciki ba."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel