Kankara: 'Yan makaranta da aka sace suna cikin koshin lafiya, Sojin Najeriya

Kankara: 'Yan makaranta da aka sace suna cikin koshin lafiya, Sojin Najeriya

- Kakakin rundunar soji, Manjo janar John Enenche, ya ce babu dalibin GSSS Kankara da ya mutu

- A cewarsa, kullum sojoji cikin sintiri suke, da an kashe wani yaro, da sun ga alamar hakan

- Enenche ya sanar da manema labarai hakan ne a ranar Laraba a hedkwatar tsaro da ke Abuja

A ranar Laraba, hedkwatar tsaro ta ce ta samu duk wasu labarai da take bukata daga bakin jami'an tsaro da kuma gwamnatin jihar Katsina, inda tace ga dukkan alamu, yaran suna hannun 'yan bindigan, kuma babu wanda ya mutu.

Kakakin hedkwatar tsaro, Manjo Janar John Enenche shine ya sanar da manema labarai hakan a hedkwatar sojoji da ke Abuja, inda yace sojoji basa cikin wadanda za su yi ciniki da 'yan ta'adda, kuma ba za su taba yi ba.

A cewarsa, har yanzu babu yaron da aka kashe, kuma jami'an tsaro suna kokarin ganin hanyar da za su bi don su kwatar yaran daga hannun 'yan ta'addan, kuma su koma wurin iyayensu lafiya, Daily Trust ta wallafa.

Kankara: 'Yan makaranta da aka sace suna cikin koshin lafiya, Sojin Najeriya
Kankara: 'Yan makaranta da aka sace suna cikin koshin lafiya, Sojin Najeriya. Hoto daga @daily_trust
Source: Twitter

KU KARANTA: Na fuskanci kalubale a 2015 saboda alheran da nake son kawowa Najeriya, Jonathan

"Babu wanda ya mutu, don har yanzu basu tsinci gawa ko sun samu labarin mutuwar wani ba. Kuma har yanzu sojoji suna cigaba da sintiri.

"A matsayin gwamnan na uba, zai yi iyakar kokarinsa wurin bin hanyar taimakon yaran."

Enenche ya kara da cewa, "A tsarin soji, babu maganar ciniki tsakaninsa da dan ta'adda. Muna yin ayyukanmu ne kai tsaye, bamu da wani dalili da zai sa mu lallaba 'yan ta'adda."

KU KARANTA: 'Yan sanda sun sake damke mutumin da yayi bidiyon da ya tada zanga-zangar EndSARS

A wani labari na daban, wani mutum wanda 'yan fashi suka kwace wa mota ya ce ya nemi taimakon 'yan sanda amma sun zolaye shi da cewa tunda har 'yan Najeriya suka bukaci a kawo karshen SARS, dole ne su fuskanci kalubale.

SARS wasu 'yan sanda ne wadanda suka addabi al'umma kafin sifeta janar na 'yan sanda, Mohammed Adamu ya rushe su.

Wasu 'yan Najeriya sun koka a kafafen sada zumuntar zamani a kan rashin tsaron da ya addabi kasa a lokacin.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel