Buhari yana da kudirin alheri ga Najeriya, Bola Tinubu

Buhari yana da kudirin alheri ga Najeriya, Bola Tinubu

- Shugaban jam'iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu, ya bayyana Buhari a matsayin shugaba nagari

- Ya ce Buhari shugaba ne wanda yake yi wa Najeriya fatan alheri da burin samun cigaba

- Ya fadi hakan ne a ranar Laraba, 17 ga watan Disamba, ranar da Buhari yake cika shekaru 78 da haihuwa

Shugaban jam'iyyar APC, kuma tsohon gwamnan jihar Legas, Asiwaju Bola Tinubu, ya bayyana shugaba Buhari a matsayin mai kaunar Najeriya, kuma shugaba nagari wanda yake yi wa kasar nan fatan samun cigaba.

A ranar Laraba, 17 ga watan Disamban 2020, ranar da Buhari ya cika shekaru 78, Tinubu ya bukaci 'yan Najeriya su baiwa shugaban hadin kai.

Kamar yadda Tinubu ya ce: "Ni da sauran 'yan kasa nagari, mun taru don mara maka baya don ka samar da cigaba da nasara, wurin cire Najeriya daga kangin da take ciki.

KU KARANTA: Kankara: Iyayen dalibai sun jeru a farfajiyar makaranta suna jiran dawowar 'ya'yansu

Buhari yana da kudirin alheri ga Najeriya, Bola Tinubu
Buhari yana da kudirin alheri ga Najeriya, Bola Tinubu. Hoto daga @daily_trust
Asali: Twitter

KU KARANTA: Kankara: 'Yan makaranta da aka sace suna cikin koshin lafiya, Sojin Najeriya

"Kai mai kishin Najeriya ne, kuma mai burin samar wa kasar nan cigaba, ina tare da kai a nan.

"Muna fatan Allah ya baka karfi da ikon tsayawa don samar wa Najeriya cigaba da zaman lafiya.

"Wajibi ne mu gode wa Allah da ya baka tsawon rai har ka ga zagayowar ranar haihuwarka."

A wani labari na daban, Gwamna Samuel Ortom na jihar Benue ya shawarci matasan jiharsa da su yaki 'yan ta'adda da 'yan fashi kada su tsaya jiran hukuma.

Gwamnan ya bayar da wannan shawarar ne bayan wasu 'yan ta'adda sun afka wa kauyen Agboughul da ke wajen Makurdi da misalin karfe 11pm, inda suka kashe wani lauya, Moses Udam, wanda fasto ne a Gospel Faith Mission, matarsa Nkechi da wani tsohon makaho, Mazugu Nyikor, mai shekaru 88.

An tsinci gawar mata da mijin, sannan sun ji wa yaran Nyikor 2, ciwo da alburusai, sannan sun tsere da kanwar faston, inda suka bukaci N200,000 a matsayin kudin fansa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: