Gafasa zai jagoranci ‘Yan Majalisan dokoki daga jam’iyyar PDP zuwa APC

Gafasa zai jagoranci ‘Yan Majalisan dokoki daga jam’iyyar PDP zuwa APC

- Ana jita-jitar cewa ‘Yan Majalisa da-dama suna shirin barin APC a Kano

- Rt. Hon. Abdulaziz Gafasa da wasu da ke tare da shi ne za su sauya-sheka

- Hakan na zuwa ne jim kadan bayan an canza shugabancin majalisar jihar

Tsohon shugaban majalisar dokokin jihar Kano wanda bai dade da yin murabus ba, Abdulaziz Gafasa ya na shirin ficewa daga jam’iyyar APC.

Mu na samun kishin-kishin daga jaridar Solacebase cewa Rt. Hon. Abdulaziz Gafasa da akalla wasu ‘yan majalisar dokoki 13 za su sauya-sheka.

Abdulaziz Gafasa da ‘yan majalisar jihar da za su bi shi, za su koma jam’iyyar PDP mai adawa, wanda ba ta da rinjaye a majalisar dokokin Kano.

Jaridar ta ce hakan na zuwa ne bayan Abdulaziz Gafasa ya sauka daga kan kujerarsa na shugaban majalisa don dole, bayan ya ji za a tsige shi.

KU KARANTA: Ganduje ya yabawa Jonathan a kan kafa makarantun Almajirai

Kawo yanzu ba mu da labarin jerin sunayen ‘yan majalisar da za su fice daga APC tare da Gafasa.

Akwai kishin-kishin din cewa ‘yan majalisa sun tsige Gafasa ne bisa zargin shi da ake yi da zama ‘dan amshin-shatan gwamna Abdullahi Ganduje.

Sabanin ya yi kamari ne a sakamakon rikicin da aka samu a jam’iyyar APC mai mulki wajen tsaida ‘yan takarar kananan hukumomi na jihar Kano.

A wani kaulin kuma Abdullahi Ganduje ya na zargin Hon. Abdulaziz Gafasa da hada kai da ‘yan adawa, don haka ya shirya yadda za a tunbuke shi.

KU KARANTA: Abin da ya sa na cirewa Sanusi II rawani - Gwamnan Kano

Gafasa zai jagoranci ‘Yan Majalisan dokoki daga jam’iyyar PDP zuwa APC
Majalisar dokoki na Kano Hoto: www.premiumtimesng.com
Asali: UGC

Ana zargin wani fitaccen ‘dan majalisa da Abdulaziz Gafasa ya dakatar a farkon bana da hannu a yunkurin tsige shi, hakan ta sa shi ya yi murabus.

A jiya kun ji 'yan majalisa 35 dake majalisar dokokin jihar Kano suka rattaba hannu domin goyon bayan tsige Kakakin majalisa da shugaban masu rinjaye.

Duk da cewa shugabannin majalisar basu bayyana dalilin da ya savsuka yi murabus ba, an fahimci cewa sun sauka da arziki ne gudun a tsige su a jiya.

Shugaban masu rinjaye, Kabiru Dashi, da mataimakinsa, Tasiu Zabainawa, sun bar mukamansu.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel