2023: Yarima ya bayyana kudirinsa na tsayawa takarar shugabancin kasa

2023: Yarima ya bayyana kudirinsa na tsayawa takarar shugabancin kasa

- Tsohon gwamnan jihar Zamfara, Sani Yarima, ya bayyana kudirinsa na tsayawa takarar shugaban kasa a 2023

- Gwamnan ya bayyana wannan kudirin nasa ne a ranar Laraba a Abuja, inda yace zai tsaya ne a karkashin jam'iyyar APC

- A cewar sanatan, babu wata yarjejeniyar da APC tayi da 'yan kudu na basu damar mulki a 2023, don haka zai tsaya tsayin-daka

Tsohon gwamnan jihar Zamfara, Sani Yarima, ya bayyana burinsa na tsayawa takarar shugaban kasa a 2023, a karkashin jam'iyyar APC, Daily Trust ta wallafa hakan.

Yarima, sanata mai wakiltar Zamfara ta yamma a majalisar tarayya, ya sanar da manema labarai kudirinsa a ranar Laraba a Abuja, inda yace yana son ya samu nasara don ya gyara rayuwar 'yan Najeriya ne.

Tsohon gwamnan ya bayyana tsananin takaicin da ya shiga bayan ganin yadda ake kashe-kashe a kasar nan duk da bakar fatara da talaucin da ke addabar 'yan Najeriya.

2023: Yarima ya bayyana kudirinsa na tsayawa takarar shugabancin kasa
2023: Yarima ya bayyana kudirinsa na tsayawa takarar shugabancin kasa. Hoto daga @daily_trust
Asali: Twitter

KU KARANTA: Tsoffin sanatoci da 'yan majalisu suna zawarcin Tinubu don shugabanci kasa a 2023

Yarima yace: "Idan ba a manta ba, a 2006, na bayyana kudirina na burin zama shugaban kasar Najeriya, bayan na mulki jihar Zamfara na shekaru 8.

"Bayan nan, na yanke shawarar janye kudirina kuma bayan nan na rike kujerar sanata sau 3.

"Yanzu kuwa, bayan na ga shugaban kasa yana kokarin karasa mulkinsa a karo na biyu, sai nace bari in ga yadda Ubangiji zai yi dani, na hakura da kara neman kujerar sanata.

"Kamar yadda ku ka gani, Najeriya tana fuskantar matsalolin tsaro da tashin hankali."

KU KARANTA: Kankara: Ku dawo mana da yaranmu maza, Okonjo Iweala ga FG

Yarima yace babu wata yarjejeniyar da 'yan APC sukayi na baiwa kudu damar mulki a 2023. Yace babu wanda ya isa ya dakatar dashi daga kudirinsa.

A wani labari na daban, NSMC ta kwatanta rashin tsaron Najeriya da rashin tsaron iyakoki, ta kara da cewa hakan ne dalilin da ya sanya Najeriya ta kasa cin nasara a kan 'yan bindiga da 'yan Boko Haram.

Ta ce matsawar gwamnatin tarayya tana son cin nasara a kan rashin tsaro ta wuraren tafkin Chadi, wajibi ne a kula kwarai, Daily Trust ta wallafa.

Wadannan suna kadan daga cikin hanyoyin da za a tsare 'yan Najeriya daga cutarwar 'yan bindiga, kamar yadda mambobin kwamitin suka tattauna don samar da tsaro a kasar nan.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel