GSSS Kankara: Muna tattaunawa da Boko Haram ta hannun Malamai inji Masari

GSSS Kankara: Muna tattaunawa da Boko Haram ta hannun Malamai inji Masari

- Gwamna ya ce Hukuma ta na tattaunawa da wadanda su ka sace Dalibai a Kankara

- Aminu Bello Masari ya bayyana haka ne da aka yi hira da shi a gidan talabijin CNN

- Kungiyar ta’addancin Boko Haram ta fito ta ce wadannan dalibai 520 suna hannunta

Mai girma gwamnan jihar Katsina, Rt. Hon. Aminu Bello Masari, ya sake yin magana game da ‘yan makarantar da aka sace a ranar Juma’a.

Aminu Bello Masari ya shaidawa ‘yan jarida cewa an yi magana da ‘yan bindigan da su ka sace wadannan yara, kuma har an fara tattaunawa.

Mai girma gwamna Aminu Masari ya ce suna tattaunawa da miyagun ne ta hannun wasu daga cikin malaman makarantar da aka yi ta’adin.

A jawabin na sa, gwamnan bai iya bayyana matsayar da gwamnati ta cin ma da ‘yan ta’addan ba.

KU KARANTA: Ana so Masari ya yi gaba wajen ceto yaran Makaranta

Aminu Masari ya yi wannan bayani ne a lokacin da CNN ta yi hira da shi a ranar Laraba, 16 ga watan Disamba, 2020 game da batun 'yan makarantar.

Kamar yadda mu ka samu labari a baya, akwai wani malamin makarantar ta GSSS Kankara wanda ya yi magana da wadanda su ka sace daliban.

Shi ma wannan Bawan Allah yana cikin wadanda su ke cikin jimami, domin kuwa har da ‘dan cikinsa a jerin ‘daliban da aka sace a ranar Juma’a.

A daidai wannan lokaci kuma hedikwatar dakarun sojojin Najeriya ta bada tabbacin cewa za ta kubuto da ‘yan makarantar da aka sace a Kankara.

KU KARANTA: Ana kukan sace yara, Buhari ya kewaye gonar shanunsa

GSSS Kankara: Muna tattaunawa da Boko Haram ta hannun Malamai inji Masari
Gwamna Aminu Masari Hoto: legit.ng
Asali: UGC

Manjo Janar John Enenche ya bayyana wannan dazu a Abuja lokacin da ya ke bayani game da kokarin da jami’an sojoji su ke yi a fadin Najeriya.

Garba Shehu, hadimin Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi maza ya yi magana lokacin da aka sace 'yan makantar, ya ba jama'a kwarin gwiwa.

A wancan lokaci, Garba Shehu ya ce kwanan nan 'yan bindiga za su zama tarihi a Najeriya.

Tun ranar Asabar Shehu ya ce rundunar soji sun zagaye wuraren da ake zargin 'yan bindigan suke, amma har yanzu babu labarin kubutarsu.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel