Daliban da aka sace na cikin daji a Zamfara, Gwamna Aminu Bello Masari

Daliban da aka sace na cikin daji a Zamfara, Gwamna Aminu Bello Masari

- Gwamna Masari ya bayyanawa manema labarai inda aka kwana game da daliban Kankara da aka sace

- Masari ya yi watsi da maganar Shekau cewa Boko Haram ta sace daliban

- Ya ce suna cikin tattaunawa da yan bindigan domin ceto yaran

Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya ce daliban makarantar GGSS Kankara da sace ranar Juma'a na cikin dajin jihar Zamfara.

Masari wanda ya bayyana hakan yayin hira da BBC Hausa daren Laraba, ya ce ya samu labarin cewa daliban na jihar Zamfara.

"Suna cikin dajin Zamfara, mun samu labarin haka." Masari yace.

Ya ce gwamnatinsa na tattaunawa da masu garkuwan domin tabbatar da cewa an saki daliban.

Masari ya bayyana cewa ya fara tattaunawa da masu garkuwa, kuma yana da tabbacin cewa za'a saki yaran.

"Muna tattaunawa da wadanda suka sace daliban kuma muna son tabbatar cewa an saki yaran," yace.

KU KARANTA: An bayyana sunaye da hotunan wasu cikin daliban da aka sace a Kankara

Daliban da aka sace na cikin daji a Zamfara, Gwamna Aminu Bello Masari
Daliban da aka sace na cikin daji a Zamfara, Gwamna Aminu Bello Masari
Asali: Twitter

KU KARANTA: Buhari ya bayar da umarnin bude iyakokin kan tudu guda hudu

A bangare guda, ranar Laraba, hedkwatar tsaro ta ce ta samu duk wasu labarai da take bukata daga bakin jami'an tsaro da kuma gwamnatin jihar Katsina, inda tace ga dukkan alamu, yaran suna hannun 'yan bindigan, kuma babu wanda ya mutu.

Kakakin hedkwatar tsaro, Manjo Janar John Enenche shine ya sanar da manema labarai hakan a hedkwatar sojoji da ke Abuja, inda yace sojoji basa cikin wadanda za su yi ciniki da 'yan ta'adda, kuma ba za su taba yi ba.

A cewarsa, har yanzu babu yaron da aka kashe, kuma jami'an tsaro suna kokarin ganin hanyar da za su bi don su kwatar yaran daga hannun 'yan ta'addan, kuma su koma wurin iyayensu lafiya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel