Bidiyon Buhari ya ziyarci shanunsa a Daura ya janyo cece-kuce

Bidiyon Buhari ya ziyarci shanunsa a Daura ya janyo cece-kuce

- Wani bidiyon shugaba Muhammadu Buhari ya karade shafukan sada zumuntar zamani

- Bidiyon ya nuna yadda Buhari ya kaiwa shanunsa ziyara a Daura, don duba lafiyarsu a wurin kiwonsu

- Bidiyon ya janyo cece-kuce, inda mutane ke cewa bai iya zuwa duba makarantar ba amma ya je duba shanunsa

Wani bidiyon shugaba Muhammadu Buhari ya yi ta yawo a kafafen sada zumuntar zamani. Bidiyon ya nuna yadda Buhari ya kaiwa shanunsa ziyara a Daura, jihar Katsina, bayan wasu sa'o'i kadan da sace daruruwan yaran makarantar GSSS Kankara.

'Yan bindiga sun sace daliban GSSS Kankara, a jihar Katsina da misalin karfe 11pm na daren Juma'a.

Bidiyon da Sahara Reporters suka wallafa a ranar Litinin, yana dauke da lokaci da kuma kwanan watan, 12 ga watan Disamban 2020, an ga Buhari da hadimansa suna zagaye wurin kiwon shanunsa.

Bidiyon Buhari ya ziyarci shanunsa a Daura ya janyo cece-kuce
Bidiyon Buhari ya ziyarci shanunsa a Daura ya janyo cece-kuce. Hoto daga @MobilePunch
Source: Twitter

KU KARANTA: UN ta magantu a kan satan 'yan makarantan Kankara, ta bada muhimmin umarni

Bidiyon ya bayyana ne washegarin da aka saci daliban, kuma shugaban kasa yana cikin jihar Katsina amma ya ki zuwa makarantar, sai dai ya tura wakilai daga Abuja suka kai ziyara makarantar don su bai wa iyayen yaran hakuri.

Mawallafin Sahara Reporters, Omoyele Sowore, ya ce alamu sun nuna cewa Buhari bai damu da matsalar da Najeriya take ciki ba, lokaci ya yi da ya kamata ya tafi.

KU KARANTA: Rashin tsaro: Farfesa ya bukaci gwamnati da ta diba mafarauta aikin tsaro

"Dalibai 600 a jihar Katsina aka sace, amma ya share su; sai kuma ga shugaban kasa ya kaiwa shanunsa ziyara, don duba lafiyarsu.

"Yakamata a ce mun gane cewa mulkin Buhari ba zai haifa mana da mai ido ba, don haka mun yanke shawarar Buhari ya tafi. #Buharimustgo," kamar yadda Sowore ya wallafa a kafar sada zumuntar zamani ta Twitter.

Daga nan ne mutane da dama suka yi ta caccakar Buhari, inda wasu suke cewa tabbas shanu sun fi rayukan mutane 600 muhimmanci a wurinsa.

A wani labari na daban, 'yan bindiga sun yi garkuwa da a kalla mutane 19 a garin Ogu da Tegina da ke karamar hukumar Rafi a jihar Neja.

Shugaban ma'aikatan shugaban karamar hukumar Rafi, Mohammed Mohammed, ya tabbatar wa da gidan talabijin din Channels faruwar lamarin a ranar Litinin.

Har kiran wasu daga cikin mazauna unguwannin don samun karin bayani a kan al'amarin, Channels TV ta wallafa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel