Sojin Najeriya sun yi wa barayin 'yan makaranta zobe a Katsina, Garba Shehu

Sojin Najeriya sun yi wa barayin 'yan makaranta zobe a Katsina, Garba Shehu

- Hadimin Shugaba Muhammadu Buhari na musamman, Garba Shehu, ya ce kwanan nan 'yan bindiga za su zama tarihi

- A cewarsa, rundunar soji ta zagaye wuraren da ake zargin 'yan bindigan suke, inda suka ceto wasu daga cikin daliban Katsina

- A cewar Shehu, yawan daliban da suka gani a wurin, sun yi kasa da yawan yadda ma'aikatan makarantar suka bayar da rahoto

Babban hadimin shugaban kasa Muhammadu Buhari na musamman, Garba Shehu, ya ce rundunar soji ta zagaye wadanda suka yi garkuwa da daliban jihar Katsina.

Shehu ya bayyana wa BBC hakan a ranar Lahadi, inda yace daliban da aka samu a hannun 'yan ta'addan sun yi kasa da yawan yadda ma'aikatan makarantar suka bayar da rahoto.

Dama a ranar Juma'a ne 'yan bindiga suka ratsa wata makarantar sakandare ta kimiyya ta gwamnati da ke Kankara, jihar Katsina, inda suka yi awon gaba da wasu dalibai. Sun sace mafi yawan daliban cikin makarantar mazan.

KU KARANTA: Masari ya bayyana yawan yara 'yan makaranta da ke hannun 'yan bindiga

Sojin Najeriya sun yi wa barayin 'yan makaranta zobe a Katsina, Garba Shehu
Sojin Najeriya sun yi wa barayin 'yan makaranta zobe a Katsina, Garba Shehu. Hoto daga @Vanguardngrnews
Asali: Twitter

A wata tattaunawa da BBC suka yi da Shehu, ya ce rundunar soji ta samu nasarar kwato yawancin yaran da 'yan ta'addan suka sace.

A cewarsa, "Kwamandojin sojojin sun tattara kawunansu a wuraren da suke zargin 'yan ta'addan suke. Sai suka zagayesu."

BBC ta ruwaito yadda ake baiwa shugaba Buhari labarai a kan kokarin da ake yi wurin ceto daliban a kowacce sa'a, saboda shugaba Buhari ya kai ziyara jihar, kamar yadda Garba Shehu yace.

"Za a karkashe 'yan ta'adda da 'yan bindiga. Kwanan nan za su zama tarihi," a cewar Garba.

A cewarsa, daliban sun ce 'yan bindiga sun tsere da 10 cikin abokan karatunsu, amma ana nan ana cigaba da bincike.

Rahotanni sun tabbatar da yadda hukumar makarantar take tuntubar iyayen don jin ko daliban sun koma gidajensu, don akwai yuwuwar sun tsere daga hannun 'yan ta'addan.

KU KARANTA: Rashin tsaro: Gwamnonin APC sun shawarci Buhari a kan bayyana a gaban majalisar tarayya

A wani labari na daban, duk daliban jihar Katsina da aka dauka za su koma gidajensu nan da sa'o'i kadan, a cewar ministan tsaro, Channels TV ta wallafa.

Ministan tsaro, manjo janar Bashir Magashi ya bayar da wannan tabbacin dangane da daliban jihar Katsina wadanda aka yi garkuwa dasu, inda yace tabbas nan da sa'o'i kadan za su koma gidajensu.

Ya tabbatar da hakan a ranar Lahadi bayan ya jagoranci shugabannin tsaro zuwa jihar Katsina don jajanta wa iyaye da malaman wadanda al'amarin ya shafa, har da gwamnatin jihar a kan garkuwa da daliban.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Tags: