Masanin tsaro ya shawarci Masari ya jagoranci jami'an tsaro, ya wuce gaba wajen nemo daliban Kankara
- Kwararre a fannin tsaro, Dakta Ona Ekhomu, ya bukaci gwamna Masari na jihar Katsina ya zama jagoran neman daliban da aka sace a Kankara
- Har yanzu an gaza cimma samun takamaiman adadin daliban da ke hannun 'yan bindigar
- A sakon da ya fitar ranar Talata, Abubakar Shekau ya ce kungiyarsa ta Boko Haram ce ta sace daliban
Wani kwararre a fannin tsaro, Dr Ona Ekhomu, ya bukaci gwamna Aminu Bello Masari na Jihar Katsina da ya shige gaba, ya zama jagora, wajen ceto ɗaliban da kungiyar 'yan ta'adda ta Boko Haram ta yi ikirarin sacewa.
Ya ce, Masari ke da babbar rawar takawa wajen ceto yaran da aka sace, kamar yadda jaridar Punch ta wallafa.
A cewar Dakta Ekhomu, "duk rana ɗaya da ta wuce, tamkar kara nesa da damar ceto wadancan yaran ne."
Ekhomu, wanda shine shugaban kungiyar samar da tsaro a masana'antu, ya bayyana haka ne ranar Litinin din da ta gabata, yayin da ya ke magana dangane da sace ɗaliban makarantar kimiyya sama da 300 a Kankara dake Katsina.
KARANTA: Babban Sufetan ƴan sanda na ƙasa ya bada umarnin baza jami'an rundunar SWAT da suka maye gurbin SARS
Kwararre a fannin tsaron ya kara da cewa, sace daliban abu ne da za'a iya hana faruwarsa tun kafin ya afku.
Ya kara da cewa, gwamnatin jiha da hukumar makaranta sun nuna sakaci sosai da ya bayar da kofar sace daliban.
KARANTA: Da ma can bai cancanta ba; a karshe, Ganduje ya bayyana dalilin tsige Sanusi
"Dole ne gwamna ya wuce gaba, amma barin abin ga jami'an tsaro na Gwamnatin tarayya ba zai haifar da ɗa mai ido ba. Tunda garkuwa da mutane ya zama ruwan dare a yankin Arewa maso yamma, jami'an tsaron yanzu sun daina mayar da hankali yadda ya kamata." A cewar Ekhomu.
A baya Legit.ng ta rawaito cewa CNG sun ce zasu yi tattaki zuwa garin Daura, mahaifar shugaban kasa, Muhamadu Buhari, domin fara zaman dirshan akan sace dalibai akalla 333 a sakandiren Kankara, jihar Katsina.
Fiye da dalibai 300 ne ake zargin cewa su na hannun 'yan bindigar da suka shiga cikin dakunansu na kwana suka yi awon gaba da su.
'Yan bindigar sun dira makarantar sakandiren kimiyya da ke Kankara da talatainin daren Juma'a zuwa duku-dukun safiyar Asabar, tare da yin awon gaba da dalibai kusan 600.
Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng