Boko Haram suna daukar Almajirai cikin tafiyarsu inji Gwamna Ganduje

Boko Haram suna daukar Almajirai cikin tafiyarsu inji Gwamna Ganduje

-Abdullahi Umar Ganduje ya na ganin Boko Haram suna cin moriyar Almajirai

-Gwamnan yace ‘Yan ta’addan suna amfani da Almajirai, ana juya masu tunani

-Ganduje ya kuma yabi irin kokarin da Jonathan ya yi wa Almajirai a Najeriya

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano ya ce ‘yan ta’addan Boko Haram suna samun sojoji daga cikin Almajiran da ake da su a Arewa.

Daily Trust ta ce Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana wannan ne wajen bikin kaddamar da littafin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan.

Mai girma Abdullahi Umar Ganduje ya na cikin wadanda suka halarci wannan taro na kaddamar da littafin da aka rubuta kan tsohon shugaban kasar.

Ab¬dul¬lahi Gan¬duje ya ce: “Babu shakka Boko Haram tana samun nasara a Najeriya ne saboda akwai tulin Almajirai da ta ke juyawa tunaninsu.”

KU KARANTA: Boko Haram sun hallaka mutanen Borno da suke gudun hijira a Nijar

Gwamnan Kano ya bayyana wannan lamari na Almajirai a matsayin babbar matsala ga kasar nan.

A jawabinsa, Dr. Ganduje ya yabi tsohon shugaban kasa Jonathan a kan inganta harkar ilmi da ya yi, musamman a wajen kafa makarantun Almajirai.

“Jonathan ya fadada, kuma ya zurfafa tsarin Almajirai, kuma muna gyara wannan shiri a Kano, muna kirkiro da wasu irin wadannan makarantu a jihar.”

Ganduje ya cigaba da cewa: “Tsarin karatun Almajiri da aka kawo, abu ne mai kyau. Domin ya taimakawa yara wajen koyar Kur’ani, babu bara lokacin.”

KU KARANTA: Masari ya bayyana inda aka kai ‘Yan Makarantar da aka dauke a Kankara

Boko Haram suna daukar Almajirai cikin tafiyarsu inji Gwamna Ganduje
Jonathan da Ganduje Hoto: @Dino_Melaye
Asali: Twitter

“Amma daga baya aka lalata tsarin, shiyasa yanzu muka samu kanmu a halin da ake ciki.” Ganduje yace ilmin addini ya wuce karatun Kur’ani kawai.

Idan za ku tuna, mun kawo rahoto cewa an kaddamar da wani littafi na Goodluck Jonathan a Abuja.

Sanata Dino Melaye ya na cikin wadanda su ka je wurin wannan biki, inda ya yi amfani da wannan damar, ya nemi afuwar tsohon Shugaban Najeriyan.

Sarkin Musulmi, Al¬haji Sa'ad Abubakar; Gwamnan Bauchi, Bala Mo¬hammed, Tan¬imu Tu¬raki da Gwamna Udom Em¬manuel sun halarci wannan biki a jiya.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng