Rashin tsaro da Korona: Jihohin Arewa 8 da suka rufe makarantunsu

Rashin tsaro da Korona: Jihohin Arewa 8 da suka rufe makarantunsu

A ranar Juma'a 11 ga wata ne 'yan bindiga suka afka GSSS Kankara da ke jihar Katsina, inda suka yi awon gaba da daruruwan dalibai makarantar, bayan isar Shugaba Muhammadu Buhari Daura, garinsa na haihuwa da sa'o'i kadan.

Haka ya jefa rudani cikin sauran jihohin dake da iyaka da jihar Katsina saboda gudun kada irin haka ya fada musu.

Saboda haka, jihohi sun kulle makarantun gwamnati da masu zaman kansu cikin gaggawa.

Legit.ng ta hararo jerin jihohin da suka kulle makarantunsu cikin makon nan:

1. Zamfara

Gwamnatin jihar Zamfara ta bada umurnin kulle dukkan makarantun jihar dake makwabtaka da jihohin Katsina da Kaduna.

Kwamishanan ilmin jihar Zamfara, Ibrahim Abdullahi, ya bayyana cewa ma'aikatarsa ta baiwa gwamnan shawaran rufe wadannan makarantu gudun kada abunda ya faru da jihar Katsina ya afka musu.

Ga jerin makarantun da gwamnatin jihar ta rufe:

GASS Zurmi,GSS Birnin Magaji,

GSSS Bayumkafi

GSS Ape

GSSS Bokuyum

GSSS Dan Sadau

GDSS Nasarawa Malayi

GDSS Gusami

GDSS Gudun Kore

GDSS Tsafe

2. Jihar Katsina

Sakamakon harin da yan bindiga suka kai makarantar sakandaren gwamnati dake karamar hukumar Kankara a jihar Katsina, gwamna Aminu Bello Masari, ya bada umurnin kulle dukkan makarantun kwanan jihar.

Gwamnan ya bada umurnin ne yayin magana da manema labarai bayan ziyarar da ya kai makarantan ranar Asabar, Vanguard ta ruwaito.

Masari ya ce a kulle makarantun kuma dalibai su koma gidajensu.

KU KARANTA: Kankara: Abubuwa 3 da Shekau ka iya bukata domin fansan daliban Katsina

Rashin tsaro da Korona: Jihohin Arewa 5 da suke rufe makarantunsu
Rashin tsaro da Korona: Jihohin Arewa 5 da suke rufe makarantunsu
Asali: UGC

3. Jihar Kaduna

Gwamnatin jihar Kaduna ta bada umarnin sake garkame makarantun jihar tare da umartarsu da su kammala jarrabawa zuwa ranar Laraba, 16 ga watan Disamban 2020.

Hakan yana zuwa ne bayan sake tasowar guguwar cutar korona a karo na biyu a fadin jihar.

A sanarwar da ma'aikatar ilimin jihar ta fitar tare da sa hannun kwamishinan ilimi, ta ce za a dakatar da dukkan koyarwa da karatu a makarantun sakandare, jami'o'i da kwalejoji da ke jihar.

4. Jihar Jigawa

Gwamnatin jihar Jigawa ta sanar da batun rufe makarantun gwamnati da masu zaman kansu na firamare da sakandare a cikin jihar.

Ta bayar da umarnin rufe duk makarantu daga ranar Talata, sakamakon cigaba da yaduwar cutar COVID-19 a kasar nan, Channels Tv ta wallafa.

Mukaddashin sakataren karamin ministan ilimin kimiyya da fasaha, na jihar, Rabiu Adamu, ya sanar da hakan ta wata takarda da ya bai wa manema labarai a Dutse, babban birnin jihar.

KU KARANTA: Gwamnatin Adamawa ta tura dalibai 60 kasar Indiya karatun injiniyanci

5. Jihar Kano

Gwamnan Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya bayar da umarnin rufe dukkan makarantun gwamnati da masu zaman kansu da ke fadin Jihar.

Gwamnatin jihar Kano ba ta bayyana dalilin rufe makarantun ba a cikin gajeriyar sanarwar da kwamishinan ilimi, Sanusi Kiru, ya fitar, kamar yadda Daily Nigerian ta wallafa.

"Mai girma gwamna ya bayar da umarnin gaggauta rufe dukkan makarantun gwamnati da masu zaman kansu ba tare da bata lokaci ba."

"Ana umartar iyayen da ke da yara a makarantun kwana su je domin dauko 'ya'yansu zuwa gida daga gobe, Laraba, 16 ga watan Disamba, 2020.

"Gwamnati ta na bayar da hakuri a bisa dukkan wani rashin jin dadi da daukan wannan mataki ya haifar," kamar yadda Daily Nigerian ta wallafa sanarwar da kwamishinan ya fitar.

6. Jihar Sokoto

Gwamnatin jihar Sokoto ta bada umurnin kulle makarantun kwana 16 dake iyaka da makwabtanta.

A jawabin da aka saki ranar Alhamis, gwamnatin ta yanke shawaran ne a taron majalisar tsaron ta bisa shawara kwamishanan ilmin makarantun firamare da sakandare, Dr Muhammad Bello Guiwa.

Ga jerin makarantun da aka kulle:

GGMSS Illela, Sultan Muhammadu Tambari Arabic Secondary School, Illela, Gamji Girls College, Rabah, Government Secondary School, Gada, Government Secondary School, Gandi da Government Secondary School, Goronyo.

Hakazalika akwai Government Secondary School, Isa, Government Secondary School Sabon Birnin Gobir, Boarding Primary School, Isa, Boarding Primary School, Balle ad makarantar kwana ta firamare, Jabo.

Sauran sune UBE Junior Secondary School, Sabon Birni, Government Secondary School, Kebbe, Government Secondary School, Tureta, Government Technical College, Binji da Olusegun Obasanjo Technical College, Bafarawa.

7. Jihar Adamawa

Gwamna jihar Adamawa,, Ahmadu Fintiri, ya bada umurnin rufe dukkan makarantun gwamnati da masu zaman kansu ranar Juma'a, 18 ga Disamba, 2020, NAN ya ruwaito.

Hakan na kunshe cikin jawabin da sakataren yada labaran gwamna, Mr Humwashi Wonosikou, ya saki ranar Juma'a a Yola.

8. Jihar Benue

Gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom, ya bada umurnin rufe dukkan makarantun kwana a jihar lokacin da ya ziyarci cibiyar tsaro ta MSCC a Makurdi, birnin jihar.

NAN ta nakalto jawabinsa da cewa ya kulle makarantun ne matsayin rigakafi daga garkuwa da dalibai.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng