Harin Kankara: Gwamna Masari ya kulle dukkan makarantun kwana a jihar Katsina
- An gano wasu daga cikin yaran da suka gudu yayinda yan bindiga suka kai hari makaranta a Katsina
- Hukumar yan sanda ta yi ikirarin ceto 200 cikin yaram
- Har yanzu ba'a san adadin daliban da suka bace ba a karamar hukumar Kankara, cewar gwamna Masari
Sakamakon harin da yan bindiga suka kai makarantar sakandaren gwamnati dake karamar hukumar Kankara a jihar Katsina, gwamna Aminu Bello Masari, ya bada umurnin kulle dukkan makarantun kwanan jihar.
Gwamnan ya bada umurnin ne yayin magana da manema labarai bayan ziyarar da ya kai makarantan ranar Asabar, Vanguard ta ruwaito.
Masari ya ce a kulle makarantun kuma dalibai su koma gidajensu.
Jawabin gwamnan ya biyo bayan maganar kwamishanan ilmin jihar, Badamasi Charanci, wanda ya ce an gano dalibai 406 bayan harin da yan bindiga suka kai makarantan.
Charanchii ya bayyana hakan ne yayin jawabi ga iyayen yaran makarantar.
Yayin tattaunawar kwamishanan da yaran da suka dawo, ya ce sun bayyana yadda suka kwana a cikin daji.
"Daliban na cigaba da dawowa, kuma bisa rahoton dake kasa yanzu, adadin daliban da suka kawo yanzu 406," Charanchi ya fadi.
"Mun tattauna da da yawa cikin yaran kuma sunce sun kwashe dare cikin daji suna takawa a kafa."
"An mika wa iyayen yaran da suka zo domin mayar da su gida."
KU DUBA: Yanzu-yanzu: Ana artabu tsakanin da yan Boko Haram a Askira Uba
DUBA NAN: Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo Olu ya kamu da cutar Korona
Mun kawo muku cewa wasu 'yan bindiga sun yi awon gaba da dumbin dalibai daga wata makarantar sakandire ta kimiyya da ke karamar hukumar Kankara a jihar Katsina.
A cewar HumAngle, 'yan bindigar sun shiga har dakin kwanan daliban tare da yin awon gaba da su da duku-dukun safiyar yau, Asabar.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng