Kankara: Abubuwa 3 da Shekau ka iya bukata domin fansan daliban Katsina

Kankara: Abubuwa 3 da Shekau ka iya bukata domin fansan daliban Katsina

Abubakar Shekau, shugaban kungiyar masu tada kayar bayan Boko Haram, a ranar Talata 16 ga Disamba, ya sanar da cewa shi yayi garkuwa da daliban makarantan sakandaren Kankara a jihar Katsina.

Haka ya jefa rudani cikin ikirarin cewa yan bindigan da suka addabi Arewa maso yamma ne suka kai wannan hari.

Duk da cewa an tura dakaru ceto wadannan yaran, masana harkokin tsaro da masu sharhi kan lamuran yau da kullum sun ce Shekau na iya sake yaran ta hanyoyi uku:

1. Kudin fansa

Masana sun ce tun da garkuwa da dalibai akayi a Kankara, da yiwuwan yan ta'addan Boko Haram su bukaci gwamnatin tarayya ta biya kudin fansa kafin su sake su.

Duk da cewa yiwuwan dawowan yaran gaba daya na da matukar wuya, idan gwamnati ta shiga tattaunawa da yan ta'addan, za ta iya biyan makudan kudi domin sake su.

2. Bukatar musayan firsinoni

Wani sharadi da masana harkokin tsaro suka bayyana bisa abubuwan da suka faru a tarihi shine, Shekau zai iya bukatar musayan wasu yan Boko Haram da aka kama da yaran.

Tun lokacin da aka fara kaiwa yan ta'addan hari a Arewa maso gabas, an damke yan Boko Haram masu yawa kuma an hallaka wasu.

3. Kamar yadda akayi da yan matan Chibok, zai iya sakin wasu, kuma ya mayar da wasu yan Boko Haram

Ana tsoron Shekau na iya shigar da yaran da aka sace cikin kungiyar Boko Haram idan aka gaza cimma matsaya.

Masana sun ce kamar yadda akayi da yan matan Chibok, wasu cikin yaran za su gudu, za'a saki wasu yayinda za'a raba wasu wurare daban-daban.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng