Gwamnatin Adamawa ta tura dalibai 60 kasar Indiya karatun injiniyanci

Gwamnatin Adamawa ta tura dalibai 60 kasar Indiya karatun injiniyanci

- Daliban jihar Adamawa 60 sun garzaya kasar Indiya domin karatun Injiniyanci

- Gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri ne ya dauki nauyin karatunsu

- Wasu yan Najeriya a kafafen sada zumunta sun ce wannan asaran kudi ne, me zai hana turasu makarantun Najeirya

Gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri, ya dauki nauyin dalibai jihar 60 domin koyan ilmin injiniyanci a kasar Indiya.

Mutane 60 da aka zaba sun tafi Indiya yanzu domin fara karatunsu.

Rahoton Northeast Reporters ya nuna cewa sun tashi daga tashar jirgin saman Yola.

"Mai girma Ahmadu Umaru Fintiri a farkon shekaran nan ya baiwa yan asalin jihar Adamawa 60 daman karatun ilimin injiyanci a kasar Indiya."

"Daliban sun tashi da safen nan daga tashar jirgin Yola kuma sun nufi Indiya." cewar jawabin.

Amma wasu yan Najeriya sun soki wannan abu da gwamnan yayi, inda suka ce me zai hana shi turasu jami'o'in Najeriya su yi karatun.

Wani matashi mai suna Donald Omang a Facebook yace: "Wannan kasar na bani mamaki. Shin yaushe zamu fara alfahari da namu. Indiya? Shin me zai hana amfani da kudin wajen inganta namu domin suyi karatu a Najeriya."

Hanif Muhd yace: "Shin me ya faru da jami'ar fasaha dake Adamawa?"

Gwamnatin Adamawa ta tura dalibai 60 kasar Indiya karatun injiniyanci
Gwamnatin Adamawa ta tura dalibai 60 kasar Indiya karatun injiniyanci Crdit: Northeast reporters
Source: Facebook

Source: Legit.ng

Online view pixel