COVID-19: Kamar Kaduna, gwamnatin Jigawa ta bada umarnin garkame makarantu

COVID-19: Kamar Kaduna, gwamnatin Jigawa ta bada umarnin garkame makarantu

- Gwamnatin jihar Jigawa ta bayar da umarnin rufe makarantun da ke fadin jihar daga ranar Talata

- Ta bayar da wannan umarnin ne bayan lura da yadda cutar take cigaba da yaduwa a jihar

- Yanzu haka, an samu mutane 14 wadanda suka kamu da cutar COVID-19 a jihar

Gwamnatin jihar Jigawa ta sanar da batun rufe makarantun gwamnati da masu zaman kansu na firamare da sakandare a cikin jihar.

Ta bayar da umarnin rufe duk makarantu daga ranar Talata, sakamakon cigaba da yaduwar cutar COVID-19 a kasar nan, Channels Tv ta wallafa.

Mukaddashin sakataren karamin ministan ilimi kimiyya da fasaha, na jihar, Rabiu Adamu, ya sanar da hakan ta wata takarda da ya bai wa manema labarai a Dutse, babban birnin jihar.

KU KARANTA: COVID-19: Gwamnatin Kaduna ta sanar da rufe dukkan makarantun jihar a karo na 2

COVID-19: Kamar Kaduna, gwamnatin Jigawa ta bada umarnin garkame makarantu
COVID-19: Kamar Kaduna, gwamnatin Jigawa ta bada umarnin garkame makarantu. Hoto daga @ChannelsTv
Asali: UGC

KU KARANTA: Hankula sun tashi a kan rashin lafiyan CJN bayan bai halarci rantsar da sabbin SAN ba

Ya shawarci iyaye da masu kula da yara da su shirya tsaf don killace yaransu a gidajensu daga ranar Laraba, musamman daliban makarantun kwana.

Ana tsaka da yaduwar cutar COVID-19 a Najeriya, an samu wasu mutane 14 wadanda suke dauke da cutar a wurare daban-daban na fadin jihar.

Cikin sababbin masu cutar, mutane 11 daga cikinsu masu bautar kasa ne da ke jihar.

A wani labari na daban, gwamnatin tarayya ta samar da wani kwamiti wanda zai dinga kulawa da tsayar da farashin man fetur.

Hakan ya biyo bayan sanar da sabon farashin mai na PMS da gwamnati tayi a makon da ya gabata, inda ta sanar da farashin a ranar Litinin.

Sanarwar ta biyo bayan taron kwamitin da gwamnatin tarayya, wanda NLC ta shirya da kungiyar kasuwanci don fitar da tsayayyen farashin man fetur.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng