Gwamnatin Tarayya ta ce aikin AKK za a karasa da bashin $2.5bn da aka karbo
- Gwamnatin Tarayya ta bayyana dalilinta na karbo aron kudi daga kasar China
- Za ayi amfani da wannan $2.5bn ne domin karasa aikin AKK na gas nan da 2023
- Ministar kudi ta ce ana sa ran a jawo karfin gas ta layin Ajaokuta-Kaduna-Kano
A ranar Talata, 15 ga watan Disamba, 2020, gwamnatin tarayya ta ce ta karbo aron kudi daga Sin ne domin aikin jawo gas da ake yi a Najeriya.
Gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta ci burin kammala jawo gas tun daga garin Ajaokuta zuwa Kaduna har jihar Kano kafin nan da 2023.
Jaridar Vanguard ta ce Ministar tattalin kudi na kasa, Zainab Ahmed, ta bayyana wannan a lokacin da ta kai ziyara zuwa inda ake aikin.
Ministar tarayyar ta bibiyi sashen wannan aiki da kamfanin Oilserv Nigeria Limited ya ke yi tsakanin Ajaokuta zuwa Abuja a ranar Talata.
KU KARANTA: Gwamnatin Najeriya ta yi alkawarin Man mota zai kara araha
Zainab Ahmed ta bayyana cewa ta na sa ran za a kammala wannan aiki a lokacin da aka tsara domin kuwa kamfanin Oilserv Nigeria sun dage.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewar Ministar, amfanin wannan aiki na kawo gas ya hada da samar da aikin yi ga matasa, sannan a buda hanyar habaka tattalin Najeriya.
Ahmed ta ce: “Mu na farin ciki da za a jawo gas daga Ajaokuta, Kaduna zuwa Kano. Aikin nan zai samar da abin yi ga matasa a bangaren nan."
"'Dan kwangilar ya na aiki mai kyau da nagarta, kuma na yabawa NNPC da ta fara kawo wannan aiki."
KU KARANTA: Masu hamayya a Majalisa ba su yarda da shugaban riko a NDDC ba
“Dole mu ka jinginar da sashen kasarmu kafin a karkare batun karbo aron kudin. Ina murna da aka gama maganar, kwanan nan za a fara raba kudin.”
Kamfen 2023: 'Yan A Mutun APC Na Bin Gida-gida Don Tallata Dan Takararsu Bola Tinubu A Wata Jahar Arewa
A baya an sa ran kammala wannan aiki na shimfidar bututun mai tsawon 614km a watanni 12 kamar yadda jaridar The Cable ta fitar da rahoto.
Wannan aiki na bututun gas mai fadin inci 40, zai rika jigilar iskar gas mai nauyin takun kafa biliyan 2.2 tun daga jihar Kogi a kowace ranar Duniya.
Bututun zai taso tun daga Ajaokuta, ya ratso birnin Abuja zuwa Neja da Kaduna sannan ya kai Kano.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng