AKK: Da zarar an gama jan layin Ajaokuta zuwa Kano, mai zai yi sauki - NNPC

AKK: Da zarar an gama jan layin Ajaokuta zuwa Kano, mai zai yi sauki - NNPC

Kamfanin man fetur na Najeriya, NNPC, ya bayyana cewa mai zai rage kudi muddin Najeriya ta kammala aikin da ake shirin fara yi daga Garin Ajaokuta zuwa Kano a bana.

A cikin wannans shekarar ake sa ran cewa Gwamnatin Najeriya za ta fara aikin jawo gas daga bakin Ajaokuta, wanda zai bullo ta Garin Kaduna, ya kuma bulle a jihar Kano.

A cewar NNPC, farashin man fetur zai yi sauki idan an karkare wannan aiki. Haka kuma man da jama’a su ke amfani da shi zai kara auki kamar yadda shugaban NNPC ya fada.

Malam Mele Kolo Kyari ya yi wannan jawani ne a Ranar Lahadin nan, 8 ga Watan Maris, a wajen wani taro da aka shirya a kasuwar Duniya da ke ci a halin yanzu a Garin Kaduna.

Shugaban kamfanin na NNPC ya ce wannan aikin gas na AKK zai samar da mai mai kyau wanda za ayi amfani da shi wajen tada kamfanonin da su ka mutu a Yankin Arewa.

A sanadiyyar wannan namijin aiki, ana sa ran cewa za a bude matatun Kaduna da sauran masana’antun da ke Garuruwan Kaduna da Kano domin a samu ayyukan yi.

KU KARANTA: An gano Ma'aikatan NNPC da su ke taimakawa tsagera wajen satar mai

AKK: Da zarar an gama jan layin Ajaokuta zuwa Kano, mai zai yi sauki - NNPC

Mele Kyari ya ce kwangilar AKK za ta taimaki kamfanonin Kaduna da Kano
Source: UGC

Idan an gama aikin AKK, za a samu gas, da kuma arahar mai wanda ke da armashi da za ayi amfani da shi wajen tada kamfanonin da su ka mutu a nan Kaduna da Kano."

A wajen taron, Kyari ya kara da cewa: “Wannan zai yi sanadiyyar samawa dinbin Matasan mu ayyukan yi” Jaridar Daily Trust ta fito da wannan rahoto a Ranar Litinin dinnan.

Shugaban kamfanin KRPC na Kaduna, Injiniya Ezekiel Osarolube shi ne ya wakilci shugaban NNPC a wajen wannan taro da aka shirya a kasuwar bajakolin shekarar bana.

A jawabin na sa, Ezekiel Osarolube, ya yabawa irin kokarin da KADCCIMA ta ke yi wajen shirya wannan taro. A karshe kuma ya kaddamar da bakin man da NNPC ta hada.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit Newspaper

Online view pixel