Frank, ‘Yan adawa a Majalisa sun soki nadin Shugaban rikon kwarya a NDDC

Frank, ‘Yan adawa a Majalisa sun soki nadin Shugaban rikon kwarya a NDDC

-Shugaban kasa ya nada sabon shugaban rikon kwarya a hukumar NDDC

-‘Yan adawa a majalisar wakilai sun ce ba za su yarda da wannan nadi ba

-Timi Frank ya yi barazanar zuwa kotu da gwamnati kan wannan magana

This Day ta ce tsohon mai magana da yawun bakin jam’iyyar APC, Timi Frank, ya yi tir da nadin sabon shugaban rikon kwarya da shugaban kasa ya yi a NDDC.

Kwamred Timi Frank ya bayyana cewa nadin da shugaban kasar ya yi bai halatta ba, domin a dokar kasa babu inda aka ambaci shugaban rikon-kwarya.

Frank ya fitar da jawabi, ya ce 'Nada shugaban riko, ‘ya na hadari, ba zai yi amfani ba, zai jagwalgwala matsalar da ta ke jibge ne a ma’aikatar NDDC.'

‘Dan adawar ya yi kira ga ‘yan majalisar dattawa na wakilai daga yankin Neja-Delta, su ki amincewa da wannan nadin mukami da shugaban kasa ya yi.

KU KARANTA: An yi sababbin Sanatoci a Najeriya

Kwamred Frank ya sha alwashin shigar da gwamnatin tarayya kotu, muddin ba a janye nadin ba.

Tsohon jigon na APC ya ce tun da Sanata Godswill Akpabio ya zama Ministan harkokin Neja-Delta, ake ganin aika-aika a ma’aikatar ta cigaban Neja-Delta.

"Idan Akpabio ya na da gaskiya bai tafka wata ta’asa ba, meyasa za a nada shugaban riko daga Akwa Ibom, wanda hakan ya saba doka a karara.” Inji Frank

A cewar Frank, dole shugaban NDDC ya fito daga Delta ko Bayelsa, sannan yace satar da ake tafkawa a NDDC za ta karu da nadin shugaban rikon-kwarya.

KU KARANTA: Dole mu fadawa Buhari gaskiya - Sanatan Borno

Frank, ‘Yan adawa a Majalisa sun soki nadin Shugaban rikon kwarya a NDDC
Shugaban kasa a Majalisa Hoto: Twitter.com/BashirAhmaad
Source: Twitter

Haka zalika marasa rinjaye a majalisar wakilai sun bayyana cewa akwai zalunci a wannan nadi.

Hon. Ndudi Elumelu a madadin sauran ‘yan adawa a majalisar, ya bukaci shugaban kasa ya yi maza ya nada shugabannin da za su sa ido a hukumar NDDC.

A daidai lokacin da ake fama da matsalar rashin tsaro a Najeriya, wata kungiyar Arewa ta shirya taro kan harkar tsaro, amma ‘Yan iskan gari sun tada hayaniya.

Wasu bata-gari da ake zargin an aiko su ne, sun je sun fatattaki kungiyar CNG yayin da ake shirin gudanar da wannan taro da za ayi domin nemawa Arewa mafita.

Rahotanni sun bayyana cewa an tsara za ayi wannan zama ne a Arewa House, jihar Kaduna.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit Nigeria

Online view pixel