Buhari zai kaddamar da aikin shimfida bututun iskar gas na AKK a ranar Talata

Buhari zai kaddamar da aikin shimfida bututun iskar gas na AKK a ranar Talata

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, a ranar Talata zai kaddamar da aikin shimfida bututun iskar gas wanda zai fara tun daga Ajaokuta ya ratsa ta Kaduna kuma ya dire a Kano.

Ana sa ran kammala wannan aiki na shimfidar bututun mai tsawon kilomita 614 cikin watanni 12 kamar yadda jaridar The Cable ta ruwaito.

Wannan aiki na bututun gas mai fadin inci 40, zai rika jigilar iskar gas mai nauyin cubic feet biliyan 2.2 a duk rana.

Bututun zai taso tun daga Ajaokuta na jihar Kogi, kuma ya ratso ta birnin Abuja zuwa Neja da Kaduna sannan ya tuke a jihar Kano.

Legit.ng ta fahimci cewa, an yi wa wannan aiki lakabi da AKK.

Shugaba Muhammadu Buhari
Hakkin mallakar hoto: Fadar shugaban kasa
Shugaba Muhammadu Buhari Hakkin mallakar hoto: Fadar shugaban kasa
Asali: UGC

Shugaban sashen hulda da al'umma na kamfanin man fetur na kasa NNPC, Kennie Obateru, shi ne ya sanar da hakan a birnin Abuja.

Ya ce shugaba Buhari zai kaddamar da aikin ne daga nesa yana zaune a fadarsa ta Aso Villa a birnin Abuja, a wani yanayi da 'yan Hausa ke kira 'mai kama-da-wane'.

Za a kaddamar da aikin ne daga yankin Rigachukun na jihar Kaduna da kuma yankin kamfanin Ajaokuta na jihar Kogi tare a lokaci guda.

Da ya ke lissafa moriya ta fuskar tattalin arziki da za a ci da wannan aiki idan an kammala, Obateru ya ce zai haɓaka samuwar makamashi a cikin gidajen al'umma.

KARANTA KUMA: Jihohi 10 da suka fi kowanne yawan mutane masu cutar korona a Najeriya

Haka kuma ya ce zai farfado da masana'antu musamman a yankunan Arewacin Najeriya.

Kaza lika ya ce zai bunkasa samun wutar lantarki da kusa megawatts 3600, wanda hakan zai taimaka wajen farfado da kamfanonin hada sutura wanda shi kadai zai samar da ayyuka fiye da miliyan 3.

Obateru ya ci gaba da cewa, ana sa ran idan an kammala shi, wannan aiki zai taimaka wajen samar da makamashin da masana'antu ke bukata musamman na takin zamani da sauransu.

Idan ba a manta ba, a shekarar 2008 ne majalisar zartarwa ta tarayya ce ta amince da wannan aiki, inda kuma gwamnatin shugaba Buhari ta ba da kwangilarsa a shekarar 2017.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng