Yanzu-yanzu: Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo Olu ya shiga killace kansa
- Bayan wata da watanni yana yaki da cutar Korona a jiharsa, gwamnan Legas ya killace kansa
- Da yiwuwan cutar Korona ta dawo kwashe mutane yayinda mutane 3000 suka kamu cikin watan Disamba
Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, zai shiga killace kansa, bayan daya daga cikin hadimansa na jiki ya kamu da cutar Korona ranar Alhamis.
Za'a yiwa gwamna Sanwo-Olu da mambobin majalisarsa gwajin cutar Korona ranar Juma'a amma zai cigaba da killace kansa kar lokacin da sakamakon ya fito.
"Muna fuskantar hauhawar adadin masu kamuwa da cutar COvID-19 a jihar Legas kuma dukkan al'ummar jihar su bi ka'idojin baiwa juna tazara, tsaftace hannu da kuma gujewa taron jama'a," kwamishanan lafiyan jihar, Akin Abayomi yace.
A cewar Abayomi, wannan ba shi bane kare na farko da za'a yiwa gwamnan Legas gwajin COVID-19.
KU DUBA: Kamfanin Atiku, INTELS, ya kori ma'akata 700, ya hanasu hakkinsu
KU KARANTA: Najeriya ta samu adadin sabbin masu cutar Coronavirus 675 ranar Alhamis
A bangare guda, gwamnatin tarayya a ranar Alhamis ta zargi Malaman addini da laifin sabawa umurninta wajen dakile yaduwar cutar Korona a fadin tarayya ta yadda suke tara jama'a a wuraren ibada.
Sakataren gwamnatin tarayya kuma shugaban kwamitin yaki da cutar, Boss Mustapha, ya bayyana hakan a hira da manema labarai a birnin tarayya Abuja.
Yace, "Mun lura cewa wasu yan Najeriya, musamman kungiyoyin addini sun cigaba da gudanar da shirye-shiryensu da ka iya kara yaduwan cutar."
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng