Sanwo-Olu ya bayyana wadanda suka yi harbe-harben Lekki

Sanwo-Olu ya bayyana wadanda suka yi harbe-harben Lekki

- Babajide Sanwo-Olu, gwamnan jihar Legas ya ce bidiyon da suka samu ya nuna sojoji ne suka yi harbin Lekki

- Kamar yadda yace, bayan kammala binciken kwamitin da ya kafa, za a tabbatar da adalci ga wadanda aka zalunta

- Gwamnan ya ce ba shi bane babban kwamandan rundunar sojin Najeriya, shi gwamnan jihar Legas ne

Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, ya ce bidiyon da aka samu ya nuna cewa rundunar sojin Najeirya ne suka yi harbe-harben Lekki toll gate a Legas.

A ranar Talata, jami'an tsaro cikin kayan aiki dauke da bindigogi sun tsinkayi toll gate inda masu zanga-zangar EndSARS suke na tsawon kwanaki 13 sannan suka tarwatsa su.

Lamarin ya kawo cece-kuce domin har da kasashen ketare sun caccaki gwamnatin Najeriya.

Tuni rundunar sojin Najeriya ta musanta aikata hakan yayin da gwamnatin tarayya tace za ta binciki aukuwar lamarin., The Cable ta ruwaito.

A yayin zantawa da CNN a ranar Litinin, Sanwo-Olu ya ce bidiyon da suka samu a jihar ya bayyana cewa jami'an tsaro sun ci zarafin jama'a.

"Mun mayar da hankali wurin yin binciken abinda ya faru da kuma wadanda suka aikata hakan. Babbu shakka sai an hukunta su," yace.

“Jama'a sun dinga sanar da cewa an kashe wadanda suka sani ko 'yan uwansu. Kwamitin binciken da muka kafa zai yi bincike kuma za mu bai wa 'yan uwan damar nuna sojojin da suka kashe jama'a.

“Ba ni bane babban kwamandan dakarun soji. Ni gwamnan jihar ne. Za a fitar da rahotanni kuma za a hukunta wadanda suka yi kisan."

KU KARANTA: Rashin imani: Yadda miji da mata suka azabtar da karamar yarinya saboda alawar N10

Sanwo-Olu ya bayyana wadanda suka yi harbe-harben Lekki
Sanwo-Olu ya bayyana wadanda suka yi harbe-harben Lekki. Hoto daga @TheCable
Asali: Twitter

KU KARANTA: An kashe jami'in kwastam a jihar Jigawa, an gudu da bindigarsa

A wani labari na daban, wata mata mai matsakaicin shekaru ta tsinke mazakutar mijinta a kan zarginsa da dirkawa wata budurwa ciki a yankin Appawa, wani bangare na karamar hukumar Lau na jihar Taraba.

Kamar yadda jaridar Leadership ta wallafa, mijin mai suna Babangida wanda aka fi sani da Bangis yana cikin shekarunsa na 30.

Ya samu miyagun raunika a mazakutarsa bayan da matarsa ta yi yunkurin tsinka masa mazakutar a ranar Lahadi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel