Hazikan soji sun damke 'yan fashi da masu taimaka musu a Zamfara

Hazikan soji sun damke 'yan fashi da masu taimaka musu a Zamfara

- Hedikwatar tsaron kasar ta ce dakarunta na rundunar Operation Hadarin Daji sun yi gagarumin nasara a kan 'yan bindiga a jihar Zamfara

- Ta ce dakarun sun kama wasu 'yan fashi bakwai da kuma masu taimaka musu guda biyar a Jihar

- Har ila yau sun yi nasarar kwato makamai a samammen da suka kai wasu kauyuka a karamar hukumar Kaura Namoda

Dakarun rundunar sojojin Najeriya na Operation Hadarin Daji sun yi nasarar kama wasu ‘yan fashi su bakwai tare da masu taimaka musu guda biyar a jihar Zamfara.

Shugaban bangaren yada labarai na rundunar tsaron, Manjo Janar John Enenche, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a yau Talata, 15 ga watan Disamba.

Ya bayyana cewa an yi kamen ne ranar Litinin, 14 ga watan Disamba, sashin Hausa na BBC ta ruwaito.

Hazikan soji sun damke 'yan fashi da masu taimaka musu a Zamfara
Hazikan soji sun damke 'yan fashi da masu taimaka musu a Zamfara Hoto: @DefenceInfoNG
Asali: Twitter

KU KARANTA KUMA: Rashin tsaro: Buhari ba Allah bane, za mu yi masa gyara a inda ya kama, In ji Kashim Shettima

Dakarun sun kuma yi nasarar kwato makamai yayin samamen da suka kai kauyukan Magizawa da Kani da Zango, Tabanni da Nasamu da ke karamar Hukumar Kaura Namoda.

Ya ce an kai farmakin ne bayan samun bayanan sirri game da zirga zirgan 'yan fashin, lamarin da ya sa suka yi nasarar kashe da dama daga cikinsu kuma wasu suka tsere da raunuka.

A wani labarin, majalisar dattawa a ranar Talata, 15 ga watan Disamba, ta gayyaci ministan tsaro, Manjo Janar Bashir Magashi mai ritaya da shugabannin tsaro da na sauran hukumomin tsaro.

An gayyace su ne domin su koro jawabai kan matakin da aka dauka don ceto daliban da aka sace na makarantar GSSS Kankara, jihar Katsina.

KU KARANTA KUMA: Yanzu-yanzu: Gwamna Matawalle ya kulle makarantun Zamfara dake makwabtaka da Katsina da Sokoto

Hakan ya biyo bayan gabatar da wani kudiri da Sanata Bello Mandiya (APC, Katsina ta Kudu) yayi, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel