Rashin tsaro: Buhari ba Allah bane, za mu yi masa gyara a inda ya kama, In ji Kashim Shettima

Rashin tsaro: Buhari ba Allah bane, za mu yi masa gyara a inda ya kama, In ji Kashim Shettima

- Sanata Kashim Shettima ya yi martani mai zafi a kan hali na rashin tsaro da kasar ke ciki

- Shettima ya ce za su yi wa Shugaban kasa Buhari gyara a inda ya kamata domin shi ba Allah bane

- Tsohon gwamnan ya kuma yi kira ga dakatar da shugabannin tsaron kasar

Tsohon gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima, ya ce Shugaban kasa Muhammadu Buhari ba Allah bane kuma za a dunga yi masa gyara a kan yadda yake tafiyar da matsalolin tsaron Najeriya.

Sanatan mai wakiltan Borno ta tsakiya ya ce tabarbarewar lamarin tsaro a arewa maso gabas ya shafe nasarorin da Shugaban kasar ya samu a yaki da Boko Haram.

Shettima, ya yi wannan furucin ne a lokacin da ya bayyana a shirin Arise TV a ranar Talata, 15 ga watan Disamba.

Rashin tsaro: Buhari ba Allah bane, za mu yi masa gyara a inda ya kama, In ji Kashim Shettima
Rashin tsaro: Buhari ba Allah bane, za mu yi masa gyara a inda ya kama, In ji Kashim Shettima Hoto: @PremiumTimesng
Asali: Twitter

Kalaman nasa na zuwa ne a daidai lokacin da ake tsaka da fargaba kan sace daruruwan dalibai da aka yi bayan yan bindiga sun kai wani hari makarantar sakandare na Kankara, jihar Katsina.

KU KARANTA KUMA: Gwamna Abdullahi Sule na Nasarawa ya garzaya kasar Amurka don ganin likita

Harin, wanda kungiyar Boko Haram ta dauki alhakin kaiwa, ya sabonta kira da ake yi na tsige shugabannin tsaro.

Sai dai fadar Shugaban kasar ta ce shugabannin tsaron za su ci gaba da zama kan kujerarsu idan dai har Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gamsu da aikinsu.

A yayin shirin wanda jaridar The Cable ta bibiya, Shettima ya ce koda dai rundunar na nuna kwazo sosai a yankin na arewa maso gabas, shugabannin tsaron sun kere amfaninsu.

“Domin yin adalci ga Muhammadu Buhari, ba wai muna dasa ayar tambaya bane a kansa, bama tantamar jajircewarsa kan halin da mutanenmu ke ciki, bama tantama a kan muradinsa na dawo da zaman lafiya a yankin arewa maso gabas,” in ji shi.

“Muna mutunta shi. Muna son sa. Amma bama kadaita shi saboda Allah kadai ake kadaitawa. Buhari ba Allah bane. Idan akwai abubuwan da ke bukatar ayi masa gyara a kai, za mu jero masa su yadda ya kamata cikin hikima.”

KU KARANTA KUMA: GSSS Kankara: Mun gano wasu Dalibai 17 da aka sace inji Gwamnan Jihar Katsina

Sanatan ya ce shugabannin tsaron sun yi iya bakin kokarinsu amma “kokarinsu ya gaza,” inda ya kara da cewa: “gaskiya, daidaito da adalci, hatta ga tunanin hankali ma sun isa su sa a nemi wadannan shugabannin tsaro su tafi.”

A wani labarin, mun ji cewa an gano yawan ‘Yan makarantar na GSSS Kankara da miyagu su ka sace. An gano adadin ne bayan wani Dalibi guda ya samu ya kubuta.

Wannan yaro mai suna Osama Aminu Maale da ya samu ya tsere yace su 520 aka sace. Alkaluman na sa ya sha banbam da na hukumomin gwamnati.

Osama Aminu Maale yace rashin lafiya ta cece sa, aka yi masa nisa, shi kuma ya samu ya tsere.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel