Majalisar dattawa ta aika sammaci ga ministan tsaro da shugabannin tsaro kan satar daliban Kankara

Majalisar dattawa ta aika sammaci ga ministan tsaro da shugabannin tsaro kan satar daliban Kankara

- Majalisar dokokin tarayya ta aika sammaci ga ministan tsaro da shugabannin tsaron kasar

- Ta mika gayyatar ne domin su zo su koro jawabai a kan matakin da aka dauka domin ceto daliban makarantar GSSS Kankara da aka sace

- A daren ranar Juma'a ne dai wasu yan bindiga suka kai farmaki makarantar tare da sace wasu dalibai

Majalisar dattawa a ranar Talata, 15 ga watan Disamba, ta gayyaci ministan tsaro, Manjo Janar Bashir Magashi mai ritaya da shugabannin tsaro da na sauran hukumomin tsaro.

An gayyace su ne domin su koro jawabai kan matakin da aka dauka don ceto daliban da aka sace na makarantar GSSS Kankara, jihar Katsina.

Hakan ya biyo bayan gabatar da wani kudiri da Sanata Bello Mandiya (APC, Katsina ta Kudu) yayi, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Majalisar dattawa ta aika sammaci ga ministan tsaro da shugabannin tsaro kan satar daliban Kankara
Majalisar dattawa ta aika sammaci ga ministan tsaro da shugabannin tsaro kan satar daliban Kankara Hoto: @BashirAhmaad
Asali: Twitter

Mandiya ya ce satar yaran na zuwa ne a daidai lokacin da ake kan lamarin satar yan matan makarantar Chibok, na jihar Borno su 270 a 2014 da kuma na Dapchi a jihar Yobe su 100 a 2018.

Ya nuna damuwa cewa idan har ba a gaggauta ceto yaran Kankara ba, makomarsu na iya shafewa a hannun yan ta’addan kamar yadda ya faru da daliban Chibok da Dapchi.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Yan majalisar wakilai biyu sun sauya sheka zuwa APC

A gudunmawa daban daban da sanatocin suka bayar, sun nuna damuwa sosai a kan ci gaban kashe kashe da sace-sacen da ke afkuwa a fadin kasar da kuma gazawar shugabannin tsaron wajen magance matsalolin.

Majalisar ta kuma bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya duba lamarin sannan ya aiwatar da shawarwarin da kwamitin majalisar kan matsalolin tsaro suka bayar.

Har ila yau ta kuma bukaci Buhari ya aiwatar da hukuncin da majalisar ta yanke a matsayin hanyoyin magance matsaloin tsaro a fadin kasar.

Shugaban majalisar dattawan, Ahmad Lawan ya bukaci yan majalisar a kan kada su gaji da tattauna lamuran tsaro.

Ya ce: “Babu abunda yafi kare rayukan mutane muhimmanci a gwamnati. Toh wannan ne ma ainahin dalilin kafa gwamnati.

“A matsayinmu na yan majalisa, kada mu taba gajiya da tattauna abunda ke faruwa da mutanenmu.

KU KARANTA KUMA: Gwamna Abdullahi Sule na Nasarawa ya garzaya kasar Amurka don ganin likita

"Mun kasance daga ccikin gwamnati amma muna da aiki na musamman. Ba bata lokacinmu muke yi ba. Mu ci gaba da magana."

A gefe guda, Kashim Shettima, ya ce Shugaban kasa Muhammadu Buhari ba Allah bane kuma za a dunga yi masa gyara a kan yadda yake tafiyar da matsalolin tsaron Najeriya.

Sanatan mai wakiltan Borno ta tsakiya ya ce tabarbarewar lamarin tsaro a arewa maso gabas ya shafe nasarorin da Shugaban kasar ya samu a yaki da Boko Haram.

Shettima, ya yi wannan furucin ne a lokacin da ya bayyana a shirin Arise TV a ranar Talata, 15 ga watan Disamba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel