Zaben Amurka: Kwalejin zabe ta tabbatar Biden ne ya ci zabe

Zaben Amurka: Kwalejin zabe ta tabbatar Biden ne ya ci zabe

- Joe Biden ya yi nasarar lashe kwallejin zabe ta Amurka bayan samun kuri'un Jihar California

- Dan takarar na jam'iyyar Democrat ya kayar da Trump a zaben watan Nuwamba ta hanyar samun kuri'u mafi rinjaye

- Wannan nasarar da Biden ya samu ta dakile duk wata dama da Trump ke da shi na kallubalantar zaben

Gumurzu da aka kwashe watanni ana yi tsakanin Shugaba Donald Trump na Amurka da zababben Shugaban kasa, Joe Biden ta zo karshe bayan Kwalejin Zaben Amurka ta tabbatar da nasarar Jam'iyyar Democrat a zaben da ta gabata.

A cewar Daily Mail, zababben shugaban kasa Joe Biden ya yi nasarar samun rinjaye a Kwalejin zaben a ranar Litinin 14 ga watan Disamba bayan nasarar da ya samu a California, wadda ta tabbatar masa da samun kwallejin zabe fiye da 270.

Zaben Amurka: Kwalejin Zabe na Amurka ta tabbatar da nasarar Biden
Zaben Amurka: Kwalejin Zabe na Amurka ta tabbatar da nasarar Biden. @JoeBiden
Asali: Getty Images

DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: Wasu da ake zargi da fashi da garkuwa sun tsere daga gidan yari

Da nasarar da ya samu a California, Biden na da kwallejin zabe 302 inda ake sa ran zai samu 306 yayin da Trump na da 232.

Zabeben shugaban kasar na Amurka, Joe Biden ya tabbatar wa Amurkawa cewa zai dawo da martabar da aka san kasar da shi.

Tun bayan zaben na ranar 3 ga watan Nuwamba, Trump ya yi ta ikirarin cewa shine ya lashe zaben sai dai ya gaza gabatar da gamsassun hujojjin da ke nuna hakan a kotu.

KU KARANTA: Bana cikin wadanda za a fara yi wa rigakafin Covid 19, in ji Shugaban Amurka, Trump

Jaridar ta ruwaito Biden na cewa zai yi wa yan kasar jawabi inda ya ce lokaci ya yi da za a bude sabon shafi a kan zaben tunda kwallejin zabe ta tabbatar shine wanda ya yi nasarar lashe zaben.

A wani labarin daban, Shugaba Muhammadu Buhari ya sauke shugaban hukumar daukan ma'aikata, Dakta Nasiru Mohammed Ladan Argungu daga mukaminsa.

Sanarwar saukewar na kunshe ne cikin wata wallafa da babban mataimakin shugaban kasa a bangaren watsa labarai, Mallam Garba Shehu ya fitar a ranar Talata kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Sanarwar ta ce Buhari ya umurci karamin ministan Kwadago da Ayyuka, Festus Keyamo, SAN, ya nada shugaban riko daga cikin manyan direktocin hukumar don maye gurbin Argungu a yanzu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel