Bana cikin wadanda za a fara yi wa rigakafin Covid 19, in ji Shugaban Amurka, Trump
- Donald Trump, shugaban ƙasar Amurka ya ce ba zai yi riga kafin kwayar cutar covid 19 ba a yanzu
- Hakan na zuwa ne sakamakon umurnin da shugaban ya bada na cewa a jinkirta bawa ma'aikatan gidan gwamnati
- Ya ce idan ba wani buƙata na dole bane ta taso yana son sai nan gaba shi da sauran ma'aikatan White House za su karbi riga-kafin
Shugaban ƙasar Amurka Donald Trump ya ce ba zai yarda a masa riga-kafin kwayar cutar Covid 19 ba a yanzu.
Jinkirin na zuwa ne saboda umurnin da ya bayar na cewa kada a bawa ma'aikatan gidan gwamnati na White House riga-kafin a yanzu.
Kamar yadda ya faɗa cikin rubutun da ya wallafa a Twitter, Trump ya ce, "bai shirya karbar riga kafin a yanzu ba sai dai nan gaba a lokacin da ya dace."
DUBA WANNAN: Hotuna: Ganduje ya tafi ta'aziyya Danbatta, ya bada N1.6m ga iyalan mutum 16 da suka rasu
"Mutanen da ke aiki a White House za su karɓi riga-kafin a nan gaba sai dai idan ya zama dole.
"Na umurci a ɗauki wannan matakan," kamar yadda ya rubuta.
Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna na Amurka, FDA, a ranar Juma'a ta amince da fara amfani da rigakafin na COVID 19 na gaggawa da kamfanin Pfizer da BioNTech suka kera.
Mutanen da shekarunsu ya dara 16 ne za iya bawa rigakafin.
A baya, mahukunta a bangaren lafiya sun ce ma'aikatan lafiya ne ya dace a fara bawa rigakafin yayin da sauran mutanen gari kuma za su samu nasu daga baya.
A wani labarin daban, Shugaba Muhammadu Buhari ya sauke shugaban hukumar daukan ma'aikata, Dakta Nasiru Mohammed Ladan Argungu daga mukaminsa.
Sanarwar saukewar na kunshe ne cikin wata wallafa da babban mataimakin shugaban kasa a bangaren watsa labarai, Mallam Garba Shehu ya fitar a ranar Talata kamar yadda The Punch ta ruwaito.
Sanarwar ta ce Buhari ya umurci karamin ministan Kwadago da Ayyuka, Festus Keyamo, SAN, ya nada shugaban riko daga cikin manyan direktocin hukumar don maye gurbin Argungu a yanzu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng