Satar yaran Kankara: Sultan ya aika gagarumin sako ga Buhari, ya yi kira ga dakatar da shugabannin tsaro

Satar yaran Kankara: Sultan ya aika gagarumin sako ga Buhari, ya yi kira ga dakatar da shugabannin tsaro

- Sultan na Sokoto ya shawarci Buhari da ya sawwake wa dukkanin shugabannin tsaro ayyukansu

- Wasu yan bindiga sun sace kimain dalibai 600 a Katsina a ranar Juma’a, 11 ga watan Disamba

- Basaraken ya bayyana cewa lamarin ya nuna gurbacewar tsarin tsaron kasar

Muhammad Sa’ad Abubakar III, Shugaban kungiyar Jama’atu Nasril Islam (JNI) kuma Sultan na Sokoto ya yi Allah wadai da sace daliban makarantar sakandare na Kankara da aka yi a jihar Katsina.

Daily Nigerian ta ruwaito cewa Sultan, a cikin wani jawabi da ya saki a ranar Litinin, 14 ga watan Disamba, ta hannun babban sakataren JNI, Khalid Aliyu, ya ce lamarin ya nuna matsaloli a tsarin tsaron Najeriya wanda akwai bukatar magance su cikin gaggawa.

Legit.ng ta tattaro cewa ya ce satar daliban ya kasance abun bakin ciki, musamman da yake zuwa a daidai lokacin da ake juyayin kisan da aka yi wa al’umma a Zabarmari.

Satar yaran Kankara: Sultan ya aika gagarumin sako ga Buhari, ya yi kira ga dakatar da shugabannin tsaro
Satar yaran Kankara: Sultan ya aika gagarumin sako ga Buhari, ya yi kira ga dakatar da shugabannin tsaro Hoto: @MBuhari
Source: Twitter

KU KARANTA KUMA: Yan majalisar Adamawa na PDP 4 za su biyo ni APC kwanan nan, Sanata Abbo

Ya yi korafin cewa karfin gwiwar da yan bindigar suka samu na aiwatar da satar daliban a ranar da Shugaban kasar ya isa jihar Katsina ya kara nuna halin da gwamnatinsa ke ciki.

Don haka kungiyar, ta bukaci Shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya amsa koken yan Najeriya na sauya fasalin tsaro da yin jawabi ga kasar.

“Akwai rade radin cewa saboda wasu dalilai na son zuciya, wasu manya a hukumomin tsaro basa so a kawo karshen rashin tsaro. Idan ba haka ba, ta yaya mutum zai yi bayani game da zirga zirgan daruruwan yan bindiga a kan Babura ba tare da an gane su ba.”

Ya bayyana cewa abunda yafi ba kungiyar JNI mamaki shine gazawar gwamnati wajen gano ainahin mafakar makiyan, gano inda karfinsu yake da kuma amfani da duk wani dama wajen kakkabe su ko durkusar da su.

KU KARANTA KUMA: Batagari dauke da muggan mukamai sun kai wa CNG hari yayin taro a kan tsaro a Kaduna

A gefe uda, mahaifiyar daya daga cikin daliban GSSS Kankara, ta ce har yanzu ba a ga fiye da dalibai 500 ba.

A cewarta, dalibin da ya tsere daga hannun 'yan bindigan ya sanar dasu cewa har an kashe 2 daga cikinsu.

Ta ce ya sanar dasu yadda 'yan bindigan suke ciyar da daliban da ganye, kuma suna dukansu kamar shanu.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel