Yan majalisar Adamawa na PDP 4 za su biyo ni APC kwanan nan, Sanata Abbo
- Jihar Adamawa na iya fuskantar tarin sauyin sheka a yan makonni masu zuwa idan har zancen Sanata Ishaku Abbo ya zama gaskiya
- Sanata Abbo wanda ya sanar da sauyin shekarsa zuwa APC tun a baya, ya ce akwai karin yan majalisa a jihar da ke shirin dawowa jam’iyyar
- Sanatan ya kuma zargi gwamnan jihar Adamawa Ahmadu Fintiri da haddasa rikice-rikice a PDP
Sanata Ishaku Abbo ya bayyana cewa wasu yan majalisa na jam’iyyar People's Democratic Party (PDP) su hudu a jihar Adamawa za su hade da shi a jam’iyyar All Progressives Congress (APC) kwanan nan.
A cewar sanatan, uku daga cikin yan majalisar sun kasance daga majalisar dokokin jihar Adamawa ne, yayinda daya kuma ya kasance dan majalisar wakilai.
Ya ce, kamar shi, yan majalisar za su bar PDP ne saboda yadda Gwamna Ahamdu Fintiri ya daburta jam’iyyar.
KU KARANTA KUMA: Hotuna daga kasaitaccen bikin auren diyar kanin Aliko Dangote Aziza da Aminu
Ya yi furucin ne yayinda yake zantawa da manema labarau ciki harda wakilin Legit.ng a karshen makon nan da ya gabata.
Abbo ya yi tunkawon cewa sauyin shekarsa zuwa APC babban kalubale ne ga PDP, inda ya kara da cewa ya koma jam’iyya mai mulki tare da manyan yan siyasa daga yankinsa irin su Titsi Ganama, Lawal Matoh, Aguwa Iliya, da sauransu.
Da yake martani kan wani jawabi daga kungiyar matasan PDP da ke barazanar yi masa kiranye kwanaki, Sanata Abbo ya ce yunkurinsu abun dariya ne.
KU KARANTA KUMA: Auren matashi dan Kano da Ba’amurkiya: Musulunci ya yarda da hakan, In ji Shehu Sani
A wani labarin, Blessing Onu Mark, diyar tsohon shugaban majalisar dattawa David Mark, a karshen mako ta yi wa daruruwan mambobi da magoya bayan jam'iyyun APGA da PDP jagora zuwa jam'iyyar APC a jihar Benue.
Blessing, yar majalisar tarayya ce da ke wakiltar mazabar Otukpo/Ohimini na jihar Benue.
The Nation ta ruwaito cewa mambobin wasu jam'iyyun siyasa a jihar suma sun sauya sheka zuwa jam'iyyar ta APC.
Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng