'Yan bindiga sun kashe 2 daga cikin daliban da suka kwashe, Dalibin da ya kubuta

'Yan bindiga sun kashe 2 daga cikin daliban da suka kwashe, Dalibin da ya kubuta

- Mahaifiyar daya daga cikin daliban GSSS Kankara, ta ce har yanzu ba a ga fiye da dalibai 500 ba

- A cewarta, dalibin da ya tsere daga hannun 'yan bindigan ya sanar dasu cewa har an kashe 2 daga cikinsu

- A cewarta, ya sanar dasu yadda 'yan bindigan suke ciyar da daliban da ganye, kuma suna dukansu kamar shanu

Daya daga cikin daliban GSSS Kankara na jihar Katsina, wanda ya samu ya tsere daga hannun 'yan ta'adda ya ce 'yan ta'addan sun kashe 2 daga cikin daliban, Vanguard ta wallafa.

Daya daga cikin iyayen yaran da ke hannun 'yan ta'addan, Faiza Hamza Kankara, ta sanar da hakan, inda tace wanda ya tsere daga hannun 'yan ta'addan ne ya sanar dasu hakan.

Matar wacce take cikin matsananciyar damuwa ta ce dalibin ya sanar dasu yadda 'yan bindigan suke ciyar dasu ganye kuma suke dukansu kamar shanu.

KU KARANTA: Mace mai dogaro da kanta bata rokon namiji, ku yi aikin hankali ku kyautata musu, Jaruma Juliet

'Yan bindiga sun kashe 2 daga cikin daliban da suka kwashe, Dalibin da ya kubuta
'Yan bindiga sun kashe 2 daga cikin daliban da suka kwashe, Dalibin da ya kubuta. Hoto daga @Vanguardngrnews
Asali: Twitter

Ta kara da cewa, dalibin ya ce har yanzu ba a ga fiye da dalibai 500 ba, kuma duk wanda yace yara 10 ne ba a gani ba, karya yake yi.

A cewarta, "Har yanzu ba a ga da na Usman Lawal Tahir ba, wanda yake a SS2.

"Daya daga cikin daliban da ya tsero jiya (Lahadi da daddare) ya ce daliban guda 520 ne, duk da 2 da aka kashe, da shi da ya tsero."

KU KARANTA: Rashin tsaro: Gwamnonin APC sun shawarci Buhari a kan bayyana a gaban majalisar tarayya

A wani labari na daban, Rundunar sojin Najeriya sun saki wasu hotuna, wadanda suke nuna miyagun makamai da suka kwace daga hannun mayakan Boko Haram lokacin wani karon batta da suka yi a arewa maso gabas a ranar 12 ga watan Disamban 2020.

Kungiyar Boko Haram sun kai wani hari zuwa karamar hukumar Askira Uba da ke arewa maso gabashin Najeriya, sai dai tarkonsu bai kama kurciya ba, a cewar sojojin.

Mataimakin shugaban jami'in hulda da jama'a na Division 7 da ke rundunar sojin Najeriya a Maiduguri, Kanal Ado Isa, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata takarda da ya fitar ranar Lahadi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel