Batagari dauke da muggan mukamai sun kai wa CNG hari yayin taro a kan tsaro a Kaduna
- Batagari dauke da muggan makamai sun kai hari a kan mahalarta taron gamayyar kungiyoyin arewa
- Matasa dauke da muggan makamai sun tarwatsa taron tare da lalata dukiyar dumbin miliyoyi
- Mahalarta taron sun hada da tsofin sojoji, tsofin 'yan sanda, shugabannin addini, da masu sarautar gargajiya
Wasu batagari kimanin su dari sun kai farmaki Arewa House, wurin taron gamayyar kun giyoyin arewa (CNG) akan yanayin tsaron yankin arewa a kwaryar birnin Kaduna.
The Nation ta rawaito cewa batagarin, wadanda ke dauke muggan makamai, sun kai hari kan mutanen da suka halarcin taron da safiyar ranar Litinin.
Bayan sun shiga harabar wurin taron dauke da makamansu tsirara a hannu, batagarin sun tafka barna tare da kwace wayoyin hannu da kwasar wasu kaya na dumbin miliyoyi.
Gamayyar kungiyoyin arewa (CNG) sun shirya taron ne domin tattauna yadda za'a kulla da gwamnati wajen shawo kan kalubalen tsaro, musamman dangane da batun ceto dalibai fiye da 300 da 'yan bindiga suka sace a Katsina.
KARANTA: Boko Haram sun kashe wani ango, sun yi amfani da wayarsa wajen sanar cewa "ni dan wuta ne"
Taron ya samu halartar tsofin sojoji, tsofin 'yan sanda, shugabannin addini, masu sarautar gargajiya, kungiyoyin mata da matasa da kungiyoyin 'yan kasuwa.
Yayin tattaunawarsa da manema shugaban CNG, Balarabe Rufai, ya bayyana harin a matsayin abin takaici, tare da bayyana wadanda suka dauki nauyin kai harin a matsayin makiyan arewa da Nigeria.
Ya kara da cewa da yawa daga cikin mahalarta taron ta taga suka bi domin gudun tsira da lafiyarsu.
KARANTA: Bidiyo: An daura auren Suleiman da Ba-Amurkiyya, Jenine, a Kano cikin annashuwa
Kazalika, kakakin kungiyar, Abdulaziz Suleiman, a cikin jawabin da ya fitar, ya ce bayan hargitsa teburan wurin taron da batagarin suka yi, sun lalata gilasan tagogi da lalata motocin mahalarta taron.
Kakakin ya jaddada manufar kungiyarsu ta tabbatar da tsaro da dawo da zaman lafiya a arewa domin jama'ar yankin su yi rayuwa cikin kwanciyar hankali.
A baya Legit.ng ta rawaito cewa CNG sun ce zasu yi tattaki zuwa garin Daura, mahaifar shugaban kasa, Muhamadu Buhari, domin gudanar da zanga-zanga a kan sace dalibai akalla 333 a sakandiren kimiyya da ke Kankara, jihar Katsina.
Har yanzu fiye da dalibai 300 ne ake zargin cewa su na hannun 'yan bindigar da suka shiga cikin dakunansu na kwana, a makarantar sakandiren kimiyyya da ke Kankara, su ka yi awon gaba da su.
Rahotanni sun bayyana cewa 'yan bindigar sun dira makarantar sakandiren kimiyya da ke Kankara, jihar Katsina, da talatainin daren Juma'a zuwa duku-dukun safiyar Asabar, tare da yin awon gaba da dalibai kusan 600.
Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng