PDP ta roki Kotu ta karbe kujerar Hon. Yakubu Dogara tun da ya sauya-sheka

PDP ta roki Kotu ta karbe kujerar Hon. Yakubu Dogara tun da ya sauya-sheka

- Jam’iyyar PDP ta kai karar Yakubu Dogara saboda ya sauya-sheka zuwa APC

- Lauyan PDP ya roki Kotu ta sa kujerar ‘Dan Majalisar a kasuwa, a shirya zabe

- Jam’iyyar adawar ta nemi Alkali ya sa Dogara ya dawo da kudin da ya ci a APC

Jam’iyyar PDP mai adawa ta dumfari babban kotun tarayya da ke garin Abuja, ta na neman a tsige Rt. Hon. Yakubu Dogara daga majalisar wakilai.

Jaridar This Day ta fitar da rahoto a ranar Litinin, 14 ga watan Disamba, 2020, cewa PDP tana so a kori Yakubu Dogara daga kujerar da yake kai.

Jam’iyyar hamayyar ta na so ‘dan majalisar na Dass, Tafawa Balewa da Bogoro na jihar Bauchi ya rasa kujerarsa ne saboda ya koma jam’iyyar APC.

Hon. Dogara ya fice daga PDP ya koma jam’iyyar APC ne bayan ya lashe zaben da aka yi a 2019.

KU KARANTA: Dogara ya dawo APC

Jam’iyyar PDP da shugabanta a jihar Bauchi, Hamza Akuyam da suka shigar da kara mai lamba FHC/ABJ/CS/1060/2020 sun gabatar da hujjojinsu.

PDP ta ce a doka, tun da Dogara ya yi watsi da jam’iyyar da ta kai shi majalisa, tunda wa’adinsa yak are, don haka ya kamata ya yi murabus daga kujerar.

Takardun kotun da aka gabatar sun bayyana cewa Lauyoyin PDP sun dogara ne da sashe na 68(1)(g) na tsarin mulki wajen rokon a kori ‘dan majalisar.

Wadanda ake tuhuma a wannan kara su ne: Yakubu Dogara, shugaban majalisar wakilai, Ministan shari’a (AGF), hukumar zabe na kasa da kuma APC.

KU KARANTA: PDP za ta yi wa Dogara kiranye?

PDP ta roki Kotu ta karbe kujerar Hon. Yakubu Dogara tun da ya sauya-sheka
Rt. Hon. Yakubu Dogara Hoto: Twitter/HouseNgr
Source: Twitter

Lauyan yace ya zama dole Dogara ya bar majalisa, kuma ya dawo da albashi da alawus da ya karba tun daga lokacin da ya canza jam’iyya zuwa yanzu.

Sannan Hamza Akuyamya bukaci a tallata kujerar tsohon shugaban majalisar, ta yadda INEC za ta sake zabe. Alkali Okon Abang ne zai saurari wannan kara.

A kwanakin baya kun ji cewa jam'iyyar APC ta ce ta daga kafa ga wanda suka shiga jam'iyyar kwanan nan, ta ce za su iya tsayawa takarar kujera a APC.

Gwamna Nasir El-Rufai na Jihar Kaduna ne ya bayyana haka wajen taron manema labarai da aka yi a sakamakon taron kwamitin zartarwar jam'iyyar APC.

Daga cikin wanda suka koma jam'iyyar akwai gwamnan Ebonyi David Umahi da Yakubu Dogara.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Online view pixel