Hon. Yakubu Dogara ya fusata PDP, Jam’iyya ta na neman yi masa kiranye

Hon. Yakubu Dogara ya fusata PDP, Jam’iyya ta na neman yi masa kiranye

Daily Trust ta ce jam’iyyar PDP a jihar Bauchi ta na shirin yi wa tsohon shugaban majalisar wakilai, Rt. Hon. Yakubu Dogara kiranye daga majalisar tarayya.

Idan ba ku manta ba, kwanan nan Yakubu Dogara ya fice daga PDP, ya sauya-sheka zuwa jam’iyyar APC mai mulkin kasa da rinjaye a majalisar dokokin tarayya.

Rahotanni sun ce wannan sauya-sheka zuwa APC a karo na biyu da Yakubu Dogara ya yi, bai yi wa jam’iyyar PDP ta reshen jihar Bauchi da uwar jam’iyya ta kasa dadi ba.

Wani daga cikin manyan PDP a Bauchi, Malam Bibi Dogo, ya ce za su nemi shugabannin majalisar wakilai su janye kujerar Yakubu Dogara.

Dogara ya na wakiltar mazabar Bogoro/Dass/Tafawa Balewa.

Bibi Dogo ya ce jam’iyyar PDP za ta bukaci a sake zaben sabon ‘dan majalisa da zai wakilci yankin.

KU KARANTA: Abin da ya sa Dogara ya koma APC - CUPP

Hon. Yakubu Dogara ya fusata PDP, Jam’iyya ta na neman yi masa kiranye
Rt. Hon. Yakubu Dogara
Asali: Twitter

“Mutanensa ba su san wani dalili mai gamsarwa da ya sa ‘dan majalisar tarayyar da za su ka zaba zai koma jam’iyyar APC ba, domin Dogara bai tuntube su kafin ya sauya-sheka ba.”

“Don haka ina kira ga shugabannin majalisa su bayyana kujerar Dogara a matsayin wanda ta fadi domin mutanen mazabarsa su yi maza su zabi sabon wakili.” Inji Bib Dogo.

Dogo ya ce saboda rashin tuntubar jama’ansa da Dogara ya yi, za su fara neman sabon ‘dan majalisa da zai maye gurbinsa domin ba za su yarda da rashin da’a ba.

Jagoran jam’iyyar mai mulki a jihar Bauchi, Dogo ya ce babu abin da wasikar Rt. Hon. Yakubu Dogara ta barin PDP ta kunsa sai kame-kame da soki-burutsu.

A cewarsa, Dogara ya rasa mafaka don haka komawarsa APC ce za ta zama jana’izarsa. Ya ce a yanzu mutane ba za su iya yarda da mutumin da bai da aiki sai canza jam’iyya ba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel