2023: Jam'iyyar APC ta sahalewa Umahi, Dogara da wasu tsayawa takara
- Jam'iyyar APC ta amincewa wanda suka shiga jam'iyyar kwanan nan da wanda su ke shirin shiga tsayawa takara
- Gwamna Nasiru El-Rufai na Jihar Kaduna ne ya bayyana haka bayan taron manema kwamitin zartarwar jam'iyyar
- Daga cikin wanda suka koma jam'iyyar akwai gwamnan Ebonyi David Umahi da Yakubu Dogara, tsohon shugaban majalisar wakilai
Kwamitin zartarwa na jam'iyyar APC mai mulki a ranar Talata ya janye sharadin takara ga wanda suka shiga ko suke shirin shiga jam'iyyar.
Sharadin zai bada damar tsayawa takara a duk wata kujerar mulki ba tare da la'akari da dadewa a jam'iyyar ba.
Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ne ya bayyana haka ga majalisa bayan kammala taron kwamitin kamar yada The Punch ta ruwaito.
DUBA WANNAN: Sojoji sun kashe yan bindiga uku a Binuwai
Ya ce, "mataki na biyu shi ne kwamitin zartarwa ya sahalewa duk wanda ya shigo jam'iyyar APC kwana kwanan nan ko wanda ya ke shirin shigowa takara.
"Da wannan mataki, sababbin yan jam'iyyar za su more yanci da jindadi zaman su cikakkun yan jam'iyya.
"Za Su samu damar tsayawa takara a jam'iyyar. Za su iya takara ba tare da bukatar sai sun dade a jam'iyya ba."
KU KARANTA: Yadda makasan mahaifina suka gano inda ya boye, dan shugaban APC da aka kashe ya magantu
Gwamnan jihar Ebonyi, David Umahi ya na cikin wanda suka shiga jam'iyyar a baya bayan nan daga jam'iyyar PDP sai kuma tsohon kakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara, shi ma ya koma jam'iyyar daga PDP.
A wani labarin daban, wani da ake zargi da garkuwa da mutane ya roki a yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataye shi saboda garkuwa da wani Tijjani Kabiru, kashe shi sannan ya birne shi a kabari mara zurfi.
Anass mai shekaru 22 ya yi garkuwa da Kabiru mai shekaru 16 a ranar 9 ga watan Janairu a Kwanar Gwarmai a garin Kwantagora da ke Karamar hukumar Bebeji na Jihar Kano a cewar 'yan sanda.
An gano cewar ya bukaci a biya shi kudin fansa har naira miliyan 1.3 da kuma katin waya na N20,000 daga mahaifin yaron, Alhaji Kabiru.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng