APC vs PDP: Cikakken sunayen wadanda suka yi nasara da wadanda suka fadi zaben cike gurbi na yan majalisa a fadin Najeriya

APC vs PDP: Cikakken sunayen wadanda suka yi nasara da wadanda suka fadi zaben cike gurbi na yan majalisa a fadin Najeriya

- Hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (EFCC) ta gudanar da zabe a wasu majalisun dokokin jiha a ranar Asabar, 5 ga watan Disamba, a fadin kasar

- Musamman jam’iyyar All Progressives Congress mai mulki da babbar jam’iyyar adawa ta Democratic Party (PDP) ne suka yi takarar kujerun

- Legit.ng ta lissafo jerin wadanda suka yi nasara da kuma wadanda suka sha kashi a zaben wanda aka kammala na majalisun jiha

KU KARANTA KUMA: Harin Kankara: Har yanzu dalibai 10 ne a hannun mas garkuwa da mutane koda dai ba a tabbatar ba, In ji Garba Shehu

APC vs PDP: Cikakken sunayen wadanda suka yi nasara da wadanda suka fadi zaben cike gurbi na yan majalisa a fadin Najeriya
APC vs PDP: Cikakken sunayen wadanda suka yi nasara da wadanda suka fadi zaben cike gurbi na yan majalisa a fadin Najeriya
Source: Original

1. Mazabar Kosofe II (Lagos)

APC - Femi Saheed (Shi ya lashe zaben)

PDP - Sikiru Alebiosu

Femi Saheed na APC ya lashe zaben da kuri’u 12,494 wajen kayar da Sikiru Alebiosu na PDP wanda ya samu kuri’u 2,068.

2. Mazabar Dass (Bauchi)

APC - Bala Lukshi (Shi ya lashe zaben)

PDP - Lawal Wundi

Bala Lukshi na APC aka kaddamar a matsayin wanda yayi nasara bayan ya samu kuri’u 12,299, inda ya lallasa Lawal Wundi na PDP wanda ya samu kuri’u 11,062.

3. Mazabar Isi-Uzo (Enugu)

APC - Ejiofor Okwor

PDP - Amaka Ugwueze (Ita ta lashe zaben)

Yar takarar PDP mace, Amaka Ugwueze ta PDP, ita ta lashe zaben inda ta kayar da babban abokin hamayyarta na APC, Ejiofor Okwor.

4. Mazabar Obudu (Cross River)

APC - Abor Adaje Godwin

PDP - Maria Godwin Akwaji (Ita ta lashe zaben)

INEC ta kaddamar da Maria Godwin Akwaji ta PDP a matsayin wacce ta lashe zaben a ranar Lahadi, 6 ga watan Disamba.

Akwaji ta samu kuri’u 32,166 yayinda babban abokin adawarta Abor Adaje Godwin na APC ya samu kuri’u 3,546 kacal.

5. Mazabar Bakura (Zamfara)

APC - Bello Dankande

PDP - Ibrahim Tukur (Shi ya lashe zaben)

An gudanar da zaben cike gurbin a Zamfara a ranar Asabar, 5 ga watan Disamba, amma aka kaddamar dashi a matsayin ba kammalalle ba bayan samun hatsaniya, zartawar kuri’u da kuma kwace akwatin zabe wanda ya kawo cikas a gudanarwar zaben.

An sake zaben a ranar Talata, 8 ga watan Disamba.

Hukumar zaben ta kaddamar da Ibrahim Tukur na PDP a matsayin wanda ya lashe zaben da kuri’u 23,874 wajen kayar da Bello Dankande na APC wanda ya samu kuri’u 16,546.

KU KARANTA KUMA: Diyar tsohon shugaban majalisa, David Mark ta koma APC

6. Mazabar Ibaji (Kogi)

APC - Egbunu Atule (Shi ya lashe zaben)

PDP - Daniel Enefola

Dan takarar APC, Egbunu Atule, ya lashe zaben da kuri’u 8,515 wajen kayar da Daniel Enefola na PDP wanda ya samu kuri’u 4,565, a bisa wani rahoto daga jaridar Premium Times.

7. Mazabar Bakori (Katsina)

APC- Ibrahim Aminu (Shi ya lashe zaben)

PDP- Aminu Magaji

Dan takarar APC, Ibrahim Aminu ya samu kuri’u 20,445 wajen kayar da babban abokin adawarsa, Aminu Magaji na PDP.

8. Mazabar Bayo (Borno)

APC- Maina Maigari (Shi ya lashe zaben)

PDP- Muhammed Danjuma

Dan takarar APC, Maina Maigari ya lashe zaben da kuri’u 25,482. Ya kayar da Muhammed Danjuma na PDP wanda ya samu kuri’u 2,249, a cewar jaridar.

9. Mazabar Nganzai (Borno)

APC- Mohammed Gajiram (Shi ya lashe zaben)

PDP- Saleh Mohammed

Dan takarar na APC, Mohammed Gajiram ya lashe zaben da kuri’u 8,885 inda ya kayar da dan takarar PDP, wanda ya samu kuri’u 240.

A wani labarin, Jihar Adamawa na iya fuskantar tarin sauyin sheka a yan makonni masu zuwa idan har zancen Sanata Ishaku Abbo ya zama gaskiya.

Sanata Abbo wanda ya sanar da sauyin shekarsa zuwa APC tun a baya, ya ce akwai karin yan majalisa a jihar da ke shirin dawowa jam’iyyar.

Sanatan ya kuma zargi gwamnan jihar Adamawa Ahmadu Fintiri da haddasa rikice-rikice a PDP.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel