Harin Kankara: Har yanzu dalibai 10 ne a hannun masu garkuwa da mutane koda dai ba a tabbatar ba, In ji Garba Shehu

Harin Kankara: Har yanzu dalibai 10 ne a hannun masu garkuwa da mutane koda dai ba a tabbatar ba, In ji Garba Shehu

- Garba Shehu ya bayar da tabbacin cewa ana nan ana kokarin ceto daliban Kankara da aka yi garkuwa da su

- Hadimin Shugaban kasa a kafofin watsa labarai ya ce an tuntubi iyaye don samun bayanai yayinda ake ci gaba da binciken kauyuka da daji

- Shehu ya kuma bayyana cewa har yanzu akwai dalibai 10 a hannun wadanda suka sace su, koda dai ba a tabbatar ba

Fadar shugaban ta kuma bayyana cewa daga cikin dalibai 300 da yan bindiga suka sace a karamar hukumar Kankara da ke jihar Katsina, dalibai 10 ne kadai ke a hannun masu garkuwan har yanzu.

Garba Shehu, babban hadimin Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya tabbatar da hakan a wani wallafa da yayi a shafin Twitter a ranar Litinin, 14 ga watan Disamba.

Ya fadi hakan ne a yayinda kasa ta dauki dumi kan sace daliban a ranar Juma’a, 11 ga watan Disamba.

Harin Kankara: Har yanzu dalibai 10 ne a hannun mas garkuwa da mutane koda dai ba a tabbatar ba, In ji Garba Shehu
Harin Kankara: Har yanzu dalibai 10 ne a hannun mas garkuwa da mutane koda dai ba a tabbatar ba, In ji Garba Shehu Hoto: @GarShehu, @OfficialPDPNig
Asali: Twitter

Shehu ya ce daliban wadanda suka dawo sun fada ma majiyar sojoji cewa 10 daga cikin yan uwansu dalibai na a hannun masu garkuwa da mutane har yanzu, inda ya jadadda matsayarsa a hira da yayi da BBC.

KU KARANTA KUMA: Yan majalisar Adamawa na PDP 4 za su biyo ni APC kwanan nan, Sanata Abbo

Sai dai ya ce “har yanzu akwai bukatar tabbatar” da ikirarin yayinda aka samu rashin daidaituwa a kan adadin daliban da aka sace da wadanda aka yi nasarar cetowa.

Garba Shehu ya kuma ce an tuntubi iyayen yaran don samun bayanai game da yaransu. Ya kara da cewa “ana bincikar jeji da kauyukan da ke makwabtaka a kokarin da ake don ceto daliban da aka sace.

“Wasu daga cikin daliban da suka dawo wadanda suka zanta da sojoji sun bayyana cewa yan bindiga sun tafi da abokan karatunsu 10. Kamar yadda na fada ma BBC, cewa har yanzu akwai bukatar a tabbatar.

KU KARANTA KUMA: Hotuna daga kasaitaccen bikin auren diyar kanin Aliko Dangote Aziza da Aminu

“Shakka babu, wannan ya sha bamban da cewa an gano lissafin sauran. Ana bincikar jeji da kauyukan da ke makwabtaka sannan an tuntubi iyaye don samun bayanai game da yayansu.”

A gefe guda, mun ji cewa har yanzu ba a ga dalibai 668 na makarantar sakandaren gwamnati ta kimiyya da ke Kankara ba, kamar yadda rajistar makarantar ta nuna.

Daya daga cikin wakilanmu, wanda ya ziyarci makarantar jiya ya tattara bayanai akan yadda al'amarin ya faru, ya ce makarantar tana da dalibai 1,074 a manya da kananun azuzuwanta.

Mazauna Kankara sun ce wani jirgin sama mai dauke da wakilan gwamnatin tarayya ya sauka a titin Katsina, jiya da daddare.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel