Auren matashi dan Kano da Ba’amurkiya: Musulunci ya yarda da hakan, In ji Shehu Sani

Auren matashi dan Kano da Ba’amurkiya: Musulunci ya yarda da hakan, In ji Shehu Sani

- Sanata Shehu Sani ya yi martani kan auren da aka kulla tsakanin matashi dan Kano da Ba'amurkiya

- Sani ya ce bambancin shekaru da ke tsakanin ma'auratan ba komai bane domin Musulunci ya yarda da haka

- Tsohon dan majalisan ya ce irin wannan aure shine zai kawo kusanci tsakanin Afrika da sauran yankunan duniya da kuma tsakanin farare da bakaken fata

A ranar Lahadi, 13 ga watan Disamba ne aka daura auren matashi dan Kano, Suleiman Isah mai shekaru 26 da amaryarsa Ba’amurkiya mai shekaru 46, Janine Sanchez Reimann.

Ma’auratan dai sun hadu ne a shafin soshiyal midiya a farkon shekarar nan lamarin da ya haddasa cece-kuce bayan ta biyo shi Najeriya don neman amincewar iyayensa.

Shehu Sani, tsohon dan majalisa mai wakiltan Kaduna ta tsakiya, wanda ya kasance cikin daukacin al’umman da suka shaidi auren, ya yi martani a kan cece-kuce da ake tayi saboda banbancin shekaru da ke a tsakanin, ma’auratan.

Auren matashi dan Kano da Ba’amurkiya: Musulunci ya yarda da hakan, In ji Shehu Sani
Auren matashi dan Kano da Ba’amurkiya: Musulunci ya yarda da hakan, In ji Shehu Sani Hoto: @thecablestyle
Asali: Twitter

KU KARANTA KUMA: Yadda jami’anmu suka kama wata babbar mota dankare da bindigogi 73 da harsasai 891 a Kebbi - Kwastam

Tsohon sanatan ya ce ya kamata auren Isah da Janine ya zama izna wajen kore shamaki da ake samu ta bangaren aure tsakanin Afrika da sauran kasashen duniya saboda kabilanci da addini, jaridar The Cable ta ruwaito.

“Aure ne da aka yarda dashi a addinin Islama. Aure ne da mutanen Hausa-Fulani na arewacin Najeriya suka yarda dashi,” in ji Sani yayinda yake jawabi ga manema labarai.

“Ya kamata ya zama abun koyi ga sauran matasa kan su sanya soyayya da addini sama da komai.

“Kada a samu matsalar banbancin shekaru a aure. Har ila yau ya kasance iri na zaman lafiya, hadin kai, aminci da fahimta tsakanin farare da bakaken fata. Tsakanin Afrika da sauran yankunan duniya. Kuma tsakanin Musulmai da Kirista.”

KU KARANTA KUMA: Dakarun Sojojin Najeriya sun ragargaji 'yan fashi a Katsina-Ala, sun kashe guda 3

A baya mun kawo cewa an daura auren matashi dan asalin jihar Kano, Suleiman Isah, da amaryarsa baturiyar kasar Amurka, Jenine Anne Reimann, a jiya, Lahadi, a wani masallaci da ke cikin barikin 'yan sanda a unguwar Panshekara Kano.

Dandazon mutane ne suka halarci wurin taron daurin auren inda suka taya ma’auratan murna.

Mahaifin ango da abokansa sun halarci daurin aure kuma sun bayyana farin cikinsu da jin dadi.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng