Bidiyo: An daura auren Suleiman da Ba-Amurkiyya, Jenine, a Kano cikin annashuwa

Bidiyo: An daura auren Suleiman da Ba-Amurkiyya, Jenine, a Kano cikin annashuwa

- A yau, Lahadi, ne aka daura aure matashi Suleiman da sahibarsa Jenine, 'yar asalin kasar Amurka

- Ballewar annobar korona ce ta kawo tsaiko a auren Suleiman da Jenine wanda aka so yinsa tun farko-farkon 2020

- A farkon shekarar nan ne Jenine ta dira a jihar Kano tun daga Amurka domin ganawa da Suleiman da shirya aurensu

An daura auren matashi dan asalin jihar Kano, Suleiman Isah, da amaryarsa baturiyar kasar Amurka, Jenine Anne Reimann, a yau, Lahadi, a wani masallaci da ke cikin barikin 'yan sanda a unguwar Panshekara Kano.

Dandazon mutane ne suka halarci wurin taron daurin auren inda suka taya ma’auratan murna.

Mahaifin ango da abokansa sun halarci daurin aure kuma sun bayyana farin cikinsu da jin dadi.

Ango da Amarya ma sun bayyana a wurin, sun yi magana da manema labarai.

Freedom Radio ta watsa yadda aka daura auren da wasu shagulgula kai tsaye.

Sashen Hausa na BBC ya rawaito cewa tsohon sanatan jihar Kaduna ta tsakiya, Kwamred Shehu Sani, ne ya bayar da auren Jenine ga waliyyan Sulaiman; wato shine waliyyinta.

Ango Suleiman ya biya N50,000 a matsayin sadakin auren Jenine, kamar yadda wani makusancinsa ya wallafa a shafinsa na tuwita.

KARANTA: Ya samu nakasa: Mayakin kungiyar Boko Haram ya fallasa gaskiyar halin da Shekau ke ciki

Bidiyo: An daura auren Suleiman da Ba-Amurkiyya, Jenine, a Kano cikin annashuwa
Bidiyo: An daura auren Suleiman da Ba-Amurkiyya, Jenine, a Kano cikin annashuwa
Asali: UGC

Barkewar annobar Korona ce ta kawo tsaiko a auren Suleiman da Jenine wanda aka shirya yinsa a farko-farkon shekarar 2020.

A farkon shekarar 2020 ne Jenine ta dira a jihar Kano don ganin masoyinta, Suleiman, a karo na farko, a zahiri, bayan haduwarsu a dandalin sada zumunta.

KARANTA: Bidiyon Sheikh Karibu Kabara: Ina ajiye da zirin gashin Annabi da aka bani kyauta shekaru 8 da suka gabata

Batun aure da soyayyar Suleiman da Jenine sun haifar da cece-kuce da surutai saboda banbance da ke tsakaninsu.

Bayan kasancewar Suleiman Bahaushe da aka haifa kuma ya ke zaune a Kano, batun banbancin shekarunsu ya zama abun surutu.

Suleiman matashi ne mai shekaru 23 da haihuwa yayi da Jenine keda shekaru 46 a duniya, wanda hakan ya nuna cewa shekarun Amarya Jenine sun ninka na angonta, Suleiman, sau biyu.

Legit.ng Hausa ta rawaito cewa masoyan biyu sun hadu ne a dandalin sada zumunta na Instagram bayan Isa ya ankarar da Jenine game da wasu da ke neman damfararta.

Daga bisani soyayya ta yi karfi tsakaninsu har Jenine ta yi tattaki zuwa Nigeria ta gana da iyayen Suleiman kuma suka amince da aurensu.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel