Yadda jami’anmu suka kama wata babbar mota dankare da bindigogi 73 da harsasai 891 a Kebbi - Kwastam
- Jami’an hukumar kwastam sun kama mutane uku kan zargin fasa kaurin muggan kayayyaki
- Daga cikin kayayyakin da aka kama akwai bindigogi kirar gida guda 73 da harsasai 891
- Kwanturola Hamisu Albashir ya bayyana kamun a matsayin babban kalubale da sigina ga wadanda ke shirin fasa kaurin kayayyaki masu hatsari zuwa cikin kasar
Hukumar kwastam na Najeriya a ranar Lahadi, 13 ga watan Disamba, ta sanar da cewa ta kama wata babbar mota dankare da muggan makamai da suka hada da bindigogi kirar gida a Kebbi.
A wata sanarwa daga jami’in hulda da jama’a na hukumar Joseph Attah, ya ce an kama babbar motar ne a hanyar Yauri, yankin ruwan Zamare da ke jihar da shinkafa yar gida.
Attah ya ce bayan nazarin kayayyakin cikin nutsuwa, sai aka gano wasu buhuhuna da aka boye a karkashin shinkafar na dauke da bindigogi kirar gida guda 73 da harsasai 891.
Ya ce a nan take aka kama mutane uku sannan ana kan gudanar da bincike kan lamarin a yanzu haka.
KU KARANTA KUMA: Hotuna: Soja ya rasu, 2 sun jigata bayan yunkurin Boko Haram na kwace Askira Uba
Da yake magana a jawabin, kwanturola na kwastam a Zone B, Hamisu Albashir, ya bayyana lamarin a matsayin nasara a yaki da fasa kaurin muggan makamai a kasar.
Ya kara da cewa wannan aiki ya kasance kalubale da sigina ga wadanda ke shirin shigo da kayayyaki masu hatsari cikin kasar ta yankin.
ya bukaci jama’a musamman masu zama a iyakokin kasar a kan su dunga bayar da muhimman bayanai da zai taimaka wajen tsaron iyakar kasar.
Jawabin ya zo kamar haka:
“Jami’an hukumar kwastam ta tarayya reshen Zone B, a yayin sintiri kan bayanan sirri da suka samu a hanyar Yauri, yankin Zamare da ke jihar Kebbi, sun kama wata babbar mota shake da shinkafa yar gida inda aka birne jakunkuna a karkashin wasu daga cikin buhuhunan shinkafar.
“Bayan binciken jakunkunan da kyau, sai aka ga cewa suna dauke ne da bindigogi kirar gida guda 73 da harsasai 891.
“A nan take aka kama mutane uku sannan aka tsare su yayinda aka fara gudanar da bincike a kan lamarin.
“Shugaban hukumar reshen Zone B, Hamisu Albashir ya bayyana nasarar a matsayin sigina ga dukkanin wadanda ke shirin shigo da muggan kayayyaki kasar ta yankin.
“Ya yi kira ga al’umma musamman mazauna iyakokin kasar da su dunga bayar da muhimman bayanai domin tsaron iyakar kasar yadda ya kamata.”
KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Mata na zanga zanga a Katsina kan satar yaran makarantar GSSS Kankara
A wani labarin, hadimin Shugaba Muhammadu Buhari na musamman, Garba Shehu, ya ce kwanan nan 'yan bindiga za su zama tarihi.
A cewarsa, rundunar soji ta zagaye wuraren da ake zargin 'yan bindigan suke, inda suka ceto wasu daga cikin daliban Katsina.
A cewar Shehu, yawan daliban da suka gani a wurin, sun yi kasa da yawan yadda ma'aikatan makarantar suka bayar da rahoto.
Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng